DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Tuesday, July 7, 2026
HomeLabaraiKu fito ku yi wa al'umma bayani kan kudaden da kuka karɓo...

Ku fito ku yi wa al’umma bayani kan kudaden da kuka karɓo ba shi – Peter Obi

Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar NDC a zaben 2027, Peter Obi, ya kalubalanci gwamnatin Shugaba Tinubu kan yadda take ci gaba da karɓar bashi, yana mai neman da ta bayyana yadda aka kashe kuɗaɗen da aka karɓo.

A cikin wata sanarwa da Obi ya fitar a shafinsa na X, ya ce gwamnatin Tinubu ta ƙara yawan bashin da ake bin Nijeriya zuwa kusan Naira tiriliyan 200 cikin shekaru uku kacal.

Obi ya bayyana cewa bayanan da ya tattara daga Ofishin kasafin kuɗi na tarayya sun nuna cewa gwamnatin Tinubu ta karɓi bashin Naira tiriliyan 11.89 tsakanin watan Janairu zuwa Satumban shekarar 2025, adadin da ya zarce abin da aka tsara na Naira tiriliyan 10.34 da kusan Naira tiriliyan 1.54.

Tsohon gwamnan jihar Anambra ya ce abin da ya fi tayar da hankali shi ne yadda aka ware Naira tiriliyan 3.10 kacal daga cikin kuɗaɗen bashin domin ayyukan raya ƙasa, wanda ya kai kashi 17.66 cikin 100 na jimillar kuɗin da aka ware wa ayyukan ci gaba.

Ya ce hakan ya bar gibin kusan Naira tiriliyan 14.48 na ayyukan raya ƙasa ba tare da samun isasshen tallafi ba, yana mai tambayar inda ragowar kuɗaɗen suka shiga.

Obi ya zargi gwamnatin da rashin bayyana gaskiya da kuma rashin bayar da cikakken bayani kan yadda ake sarrafa kuɗaɗen da ake karɓa a matsayin bashi, yana mai cewa ya kamata gwamnati ta yi wa ‘yan Nijeriya bayani dalla-dalla.

Ya kuma yi tambaya kan ko an kashe ragowar kuɗaɗen ne wajen gudanar da harkokin yau da kullum na gwamnati ko kuma an karkatar da su zuwa wasu ayyuka daban.

Dan takarar shugaban kasar ya ce miliyoyin ‘yan Nijeriya na cikin damuwa kan yadda bashin ƙasar ke ƙaruwa cikin sauri, yana mai jaddada cewa gwamnati na da alhakin bayyana yadda ake amfani da dukiyar al’umma.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata