Kungiyar masu rajin kafa ƙasar Biafra ta IPOB ta bayyana dakatar da wasu manyan mukamai guda biyu da shugaban ƙungiyar da ake tsare da shi, Nnamdi Kanu, ya riƙe a baya, kamar yadda wata sanarwa da kafafen yaɗa labarai na cikin gida suka fitar ta rawaito.
A cewar rahotannin, ƙungiyar ta sanar da dakatar da ofishin shugaban ƙungiyar (Office of the Leader) da kuma mukamin daraktan rediyon Biafra (Director of Radio Biafra) har sai baba-ta-gani.
IPOB ta ce an ɗauki wannan mataki ne domin kare ƙungiyar, mambobinta da kuma manufofinta na dogon lokaci.
Ta ƙara da cewa manufar matakin ita ce hana wasu mutane ko ƙungiyoyi amfani da mukaman da Kanu ya riƙe a baya wajen gudanar da ayyukan da ƙungiyar ba ta amince da su ba, kamar yadda rahotannin suka bayyana.
