DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Tuesday, July 7, 2026
HomeLabaraiBa mu yi alkawarin kawo wa Nijeriya sauyi cikin dare ɗaya ba...

Ba mu yi alkawarin kawo wa Nijeriya sauyi cikin dare ɗaya ba – Akpabio

Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, ya ce gwamnatin shugaba Bola Ahmed Tinubu ba ta yi wa ‘yan Nijeriya alkawarin samar da mafita cikin dare ɗaya ba, sai dai ta yi alkawarin aiwatar da sauye-sauye masu tushe da za su haifar da ci gaba mai dorewa.

Akpabio ya bayyana haka ne yayin da yake wakiltar shugaba Tinubu a wajen kaddamar da wani titi mai tsawon kilomita bakwai da aka gina kusa da filin sauka da tashin jirage na Nnamdi Azikiwe da ke Abuja, kamar yadda gidan talabijin na Channels ya ruwaito.

Ya ce sauye-sauyen da gwamnatin ke aiwatarwa na bukatar lokaci kafin amfaninsu ya bayyana, yana mai jaddada cewa gwamnati na ci gaba da kokarin inganta tattalin arziki da rayuwar al’umma.

A cewarsa, manufar gwamnatin ita ce shimfida tubalin ci gaba mai dorewa da zai amfani ‘yan Nijeriya a nan gaba, ba wai yanzu yanzu ba.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata