DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Tuesday, July 7, 2026
HomeSiyasaMajalisar Dattawa ta fara kaɗa Ƙuri'a kan ƙudirin kafa ƴan sandan jihohi

Majalisar Dattawa ta fara kaɗa Ƙuri’a kan ƙudirin kafa ƴan sandan jihohi

Majalisar Dattawa ta yanke shawarar amfani da tsarin kaɗa ƙuri’a ka tsaye wajen kudirin kafa ‘yan sandan jihohi, bayan na’urar zaɓe ta yanar gizo da aka tanada ta samu matsalar aiki.

An ɗauki wannan mataki ne bayan nuna damuwa cewa wasu sanatoci za su iya rasa damar kaɗa ƙuri’arsu idan aka ci gaba da amfani da na’urar da ke fama da matsala.

A karkashin sabon tsarin, kowane sanata zai tashi tsaye, ya bayyana sunansa, sannan ya fito fili ya bayyana matsayinsa kan kudirin kafa ‘yan sandan jihohi.

Jagoran Majalisar Dattawa, Sanata Opeyemi Bamidele, ne ya gabatar da ƙudirin amfani da kaɗa ƙuri’ar kai tsaye, yayin da Jagoran marasa rinjaye na majalisar Sanata Abba Moro, ya mara masa baya.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata