Fitaccen malamin addinin Musulunci a Nijeriya, Sheikh Ahmad Abubakar Gumi, ya bayyana cewa babu laifi idan malamai suka shiga harkokin siyasa, yana mai cewa hakan ya fi su zauna a gefe suna yi wa ƴan siyasa addu’o’in samun nasara kawai.
Gumi ya bayyana hakan ne a wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na Facebook, yayin da ake ci gaba da muhawara kan ko ya dace malaman addini su shiga siyasa ko kuma su takaita aikinsu ga wa’azi da koyar da addini.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa muhawarar ta ƙara ɗaukar hankali ne bayan wasu fitattun malaman addinin Musulunci suka fara shiga siyasa tare da bayyana aniyarsu ta tsayawa takara a babban zaɓen shekarar 2027.
Daga cikin waɗannan malamai akwai tsohon Ministan sadarwa da tattalin arzikin zamani, Sheikh Isa Ali Ibrahim Pantami, da kuma malamin Sokoto, Sheikh Bashir Ahmad Sani, wanda ya bayyana aniyarsa ta neman kujerar gwamnan jihar Sokoto a zaɓen 2027.
Haka kuma akwai wasu malamai da dama da suka taɓa rike muƙaman siyasa ko kuma suke ci gaba da rike su a matakai daban-daban na gwamnati, lamarin da ya janyo ra’ayoyi mabambanta tsakanin al’ummar Musulmi, musamman a Arewacin Nijeriya.
Masu adawa da shigar malamai cikin siyasa na ganin cewa siyasa cike take da rikici, cin mutunci da zage-zage, abin da ka iya rage daraja da martabar malamai a idon jama’a.
A cewarsu, ya fi dacewa malamai su ci gaba da ba da wa’azi, shawarwari da kuma jan hankalin shugabanni daga wajen gwamnati maimakon su shiga takarar siyasa kai tsaye.
Sai dai masu goyon bayan ra’ayin suna cewa ba za a samu sauyi ba idan masu ilimi da gaskiya suka tsaya a gefe.
Sun ce idan malamai na da ilimi, ƙwarewa da nagarta, babu abin da zai hana su shiga siyasa domin ba da gudummawarsu wajen gyara al’amuran ƙasa.
Muhawarar ta sake ɗaukar sabon salo ne bayan fitowar Sheikh Isa Ali Ibrahim Pantami a matsayin ɗan takarar gwamna na jam’iyyar PDP a jihar Gombe gabanin zaɓen 2027.
Da yake bayyana matsayinsa, Sheikh Gumi ya ce, “Malamin addini da ya shiga siyasa ya jure wahalhalunta ya fi wanda yake zaune a kan darduma yana yi wa ’yan siyasa addu’a.”
Ya ce malamai bai kamata su guji shiga siyasa ba idan hakan zai ba su damar kawo gyara da inganta shugabanci a ƙasa.
