Kotun Tarayya da ke Abuja ta dage sauraron karar da Nafiu-Bala Gombe ya shigar, inda yake neman a hana shugabancin jam’iyyar ADC, karkashin jagorancin David Mark, ci gaba da bayyana kansu a matsayin shugabannin jam’iyyar har zuwa ranar 28 ga Satumba.
Kotun ta sanya ranar yau domi sauraron dukkan wasu bukatun da ake gabatarwa a gaban ta, amma ba a samu damar ci gaba da sauraron karar ba saboda alkalin da ke jagorantar shari’ar, Mai Shari’a Peter Lifu, bai zauna ba.
Daga bisani, kotun ta sanya ranar 28 ga Satumba domin ci gaba da sauraron karar.
A ranar 16 ga Yuni ne Mai Shari’a Lifu ya sanya ranar sauraron dukkan bukatun da aka gabatar a karar, bayan da ya yi watsi da bukatar da aka gabatar na neman ya janye daga sauraron karar.
Alkalin ya bayyana cewa bukatun guda biyu da jam’iyyar ADC da Ogbeni Rauf Aregbesola, wadanda su ne wadanda ake kara na farko da na uku, suka gabatar, ba su da hujjar da za ta sa a amince da su. Saboda haka, ya ci tarar ADC da Aregbesola naira miliyan daya kowannensu, a biya Nafiu-Bala Gombe.
ADC da Aregbesola sun gabatar da bukatu daban-daban ga Mai Shari’a Lifu, inda suka nemi ya janye daga sauraron karar da Nafi’u Gombe, wanda dan jam’iyyar ne da ke adawa da wasu matakan shugabancin jam’iyyar, ya shigar. Sun kafa bukatarsu ne kan zargin cewa alkalin na nuna son kai.
Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya (NAN) ya ruwaito cewa Gombe, a cikin karar da ya shigar, yana neman kotu ta bayar da umarnin hana David Mark, Aregbesola da sauran mambobin kwamitin gudanarwa na rikon kwarya na kasa (NWC) ci gaba da bayyana kansu a matsayin shugabannin jam’iyyar.
Ya ce yadda David Mark, Aregbesola da sauran mambobin kwamitin NWC na rikon kwarya suka zama shugabannin jam’iyyar ya saba wa tanade-tanaden kundin tsarin mulkin jam’iyyar da kuma dokar zabe.
Gombe ya maka ADC, David Mark, Aregbesola, Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) da Ralph Nwosu a matsayin wadanda ake kara na farko zuwa na biyar, a karar mai lamba FHC/ABJ/CS/1819/2025.
Ralph Nwosu shi ne tsohon shugaban jam’iyyar ADC na kasa, wanda ya sauka daga mukaminsa domin bai wa shugabancin jam’iyyar karkashin David Mark damar karbar ragamar tafiyar da jam’iyyar.
Kotun Tarayya ta dage sauraron karar ADC zuwa 28 ga Satumba