DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Wednesday, May 20, 2026
HomeWasanniMourinho na dab da komawa Real Madrid

Mourinho na dab da komawa Real Madrid

Rahotanni daga kafofin yada labarai daban-daban sun bayyana cewa kocin dan kasar Portugal, José Mourinho, na dab da komawa kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid bayan cimma yarjejeniya ta baki da kungiyar.

Rahotannin sun ce an amince da sharuddan kwantiragin shekara biyu tsakanin Mourinho da kungiyar ta kasar Sifaniya, yayin da ake jiran kammala takardun yarjejeniya da sanya hannu a kai.

Shahararren dan jaridar wasanni Fabrizio Romano ya wallafa a shafinsa na X cewa Mourinho zai tafi birnin Madrid bayan wasan karshe na La Liga tsakanin Real Madrid da Athletic Bilbao domin kammala sauran matakai kafin sanarwa a hukumance.

Romano ya ce, “An cimma dukkan sharudda tsakanin José Mourinho “The Special One” kamar yadda ake kiran sa da Real Madrid ta baki, ana jiran sanya hannu a takardu. Ana sa ran zai tafi Madrid bayan wasan Real da Bilbao”.

Idan aka tabbatar da hakan, wannan zai zama karo na biyu da Mourinho zai jagoranci Real Madrid bayan zaman da ya yi a kungiyar daga 2010 zuwa 2013.

A wa’adinsa na farko, Mourinho ya lashe gasar La Liga, Copa del Rey da kuma Spanish Super Cup tare da kungiyar.

Har yanzu Real Madrid ba ta fitar da wata sanarwa a hukumance ba kan batun, amma magoya bayan kungiyar sun fara nuna farin ciki da yiwuwar dawowar tsohon kocinsu.

Ana sa ran kungiyar za ta bayyana matsayinta a cikin kwanaki masu zuwa bayan kammala dukkan matakan yarjejeniyar.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata