DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Monday, April 20, 2026
HomeLabaraiN1.46bn aka bai wa sojoji na sayen makamai a fiye da N20bn...

N1.46bn aka bai wa sojoji na sayen makamai a fiye da N20bn da aka ware cikin kasafin kuɗin 2025 – Rahoto

Rahotanni sun nuna cewa rundunar sojin ƙasa ta Nijeriya ta samu ƙasa da kashi 10 cikin 100 na kuɗin da aka ware domin sayen kayan aikin tsaro a cikin kasafin kuɗin shekarar 2025, lamarin da ke ƙara jefa damuwa kan yadda ake yaƙi da matsalar tsaro a ƙasar.

Bayanan da aka fitar daga shafin bayanan kudin gwamnati sun nuna cewa daga cikin Naira biliyan 20.56 da aka ware domin sayen kayan tsaro, rundunar ta samu kusan Naira biliyan 1.46 kacal, wanda ke daidai da kashi 7.11 cikin 100 na kasafin.

Rahoton ya ƙara da cewa wasu sassan da suka shafi sayen manyan kayan yaƙi sun fi shan wahala, inda daga cikin Naira biliyan 336.76 da aka ware domin kayan tsaro, an fitar da kusan kashi 4.96 ne kawai.

Haka kuma, fannoni kamar gyaran kayan aiki, horo, da kuma mai na motocin soja sun samu ƙarancin kuɗi sosai, kamar yadda DailyTrust ta ruwaito.

A bangaren rundunar sojin sama, rahoton ya nuna irin wannan matsala ta ƙarancin kuɗi, inda wasu muhimman ayyuka kamar gyaran jiragen yaƙi da sayen kayan aiki suka samu ƙarancin kason kuɗi, lamarin da ke iya shafar ayyukansu na yaƙi da ta’addanci.

Masana tsaro sun bayyana cewa wannan gibi a kuɗaɗe na iya rage ƙarfin rundunonin tsaro wajen tunkarar ‘yan ta’adda da sauran masu aikata laifuka.

Sun kuma danganta hakan da yawaitar hare-hare da asarar rayuka da aka samu a wasu sassan ƙasar a cikin shekarar 2025.

Haka zalika, wasu masana sun buƙaci gwamnati ta ƙara himma wajen sakin kuɗaɗen da aka ware, tare da tabbatar da gaskiya da inganci a tsarin sayen kayan tsaro, domin bai wa jami’ai damar gudanar da ayyukansu yadda ya kamata.

 

 

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata