Hukumar Alhazan Nijeriya (NAHCON) ta buƙaci masu niyyar zuwa aikin Hajjin shekarar 2027 da su fara biyan kuɗin kafin alƙalami na Naira miliyan 5, domin tabbatar da gurabensu da kuma sauƙaƙa shirye-shiryen aikin Hajji, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.
A cikin wata sanarwa da hukumar ta fitar, ta bayyana cewa biyan kuɗin tun da wuri zai bai wa masu niyyar zuwa Hajji damar tabbatar da gurabensu, tare da rage musu nauyin kuɗin tafiya ta hanyar biyan kuɗi a matakai daban-daban.
Hukumar ta ce wannan tsari zai kuma ba ta damar fara shirye-shiryen samar da masauki da sauran hidimomin da ake buƙata cikin lokaci domin gudanar da aikin Hajjin cikin inganci.
NAHCON ta kuma sanar da fara karɓar kuɗin kafin alƙalami ga masu shirin zuwa aikin Hajjin shekarun 2028, 2029 da 2030, domin ba su damar fara tanadi tun yanzu.
Hukumar ta buƙaci masu sha’awar zuwa Hajji su fara ajiyar kuɗinsu ta hannun hukumomin jin daɗin alhazai na jihohi, ko kuma ta bankunan da aka amince da su a ƙarƙashin tsarin Hajj Savings Scheme.
A halin da ake ciki, hukumomin jin daɗin alhazai na jihohin Kwara da Taraba sun buƙaci masu niyyar zuwa Hajjin 2027 su kammala biyan kuɗinsu da cika duk wasu takardun da ake buƙata kafin ranar 26 ga Satumba, 2026, wadda NAHCON da hukumomin Saudiyya suka sanya a matsayin wa’adin ƙarshe.
Sakataren hukumar alhazai ta jihar Kwara, Abdulsalam Abdulkadir, ya ce jinkirin biyan kuɗi ko cika takardu na iya janyo tsaiko wajen samun bizar zuwa Saudiyya, wanda zai iya hana wasu damar gudanar da aikin Hajjin.
Ya tunatar da cewa a shekarun baya wasu maniyyata sun rasa damar zuwa Hajji saboda jinkirin kammala biyan kuɗi da takardunsu, yayin da wasu suka nemi a mayar musu da kuɗinsu bayan wa’adin ya wuce.
Shi ma mukaddashin Sakataren Hukumar Alhazai ta jihar Taraba, Alhaji Abubakar Usman Tanko, ya bayyana cewa masu niyyar zuwa Hajji daga jihar za su fara biyan Naira miliyan 7 a matsayin kuɗin farko.
Ya ce hukumar ta Taraba ta shirya gudanar da gangamin wayar da kan jama’a a faɗin jihar domin sanar da masu niyyar zuwa Hajji sabbin ƙa’idoji da dokokin da gwamnatin Saudiyya ta shimfiɗa.
Tanko ya ƙara da cewa hukumar ta himmatu wajen tabbatar da gudanar da Hajjin 2027 cikin nasara, yana mai tunatar da cewa mahajjata 714 daga Taraba sun gudanar da Hajjin 2026, duk da cewa mutum ɗaya ya rasu, yayin da wani kuma ya rasa hannu sakamakon hatsarin mota kafin tashinsa zuwa ƙasa mai tsarki.
