DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Tuesday, September 22, 2026
HomeLabaraiNijeriya na bukatar dala biliyan 10 duk shekara domin samar da isashshen...

Nijeriya na bukatar dala biliyan 10 duk shekara domin samar da isashshen wutar lantarki – Ministan lantarki Adelabu.

By Salim Muhammad Gali

Ministan wutar lantarki na kasa Adebayo Adelabu, ya bayyana cewa Nijeriya na buƙatar aƙalla dala biliyan 10 duk shekara na tsawon shekaru 20, domin samar dai isashshen wutar lantarki ga ‘yan kasar.

Gidan talabijin na Channels ya ruwaito ministan na wannan bayanin, a yayin da yake kaddamar da tashar samar da wutar lantarki daga hasken rana mai ƙarfin megawat 2.5 a makarantar sojoji NDA da ke jihar Kaduna.

Ministan ya ce sama da shekaru 60 matsaloli sun dabaibaye bangaren lantarki da suna hada rashin isasshen saka hannun jari, rashin kiyaye kayayyakin aiki, da kuma ƙarancin inganta tsarin rarraba wutar.

Adelabu ya bayyana cewa sanya hannu kan dokar makamashi ya bai wa jihohi damar taka rawa kai tsaye a harkar samar da wuta, kama daga samarwa zuwa rabawa, kuma fiye da jihohi 11 sun fara daukar hanya.

Ukashatu Wakili
Ukashatu Wakilihttps://dclhausa.com
Ukashatu Wakili is a journalist and media professional serving as Deputy Managing Editor and Internship Coordinator at DCL Hausa. He has extensive experience in broadcast and digital journalism, with expertise in news reporting, editorial production, newsroom coordination and journalist training. He holds a B.Sc. in Mass Communication from Usmanu Danfodiyo University, Sokoto.
RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata