Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar NDC, Peter Obi, ya yi Allah-wadai da ɗabi’ar danganta laifuka da wata ƙabila baki ɗaya, yana mai cewa laifi ba ya da ƙabila kuma bai kamata a riƙa hukunta al’umma saboda laifin wasu tsiraru ba.
Obi ya bayyana hakan ne a wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na X, inda ya ce mutane da dama a Nijeriya sun sha fuskantar wariya saboda asalinsu na ƙabila maimakon a yi la’akari da halayensu da ayyukansu.
Tsohon gwamnan jihar Anambra ya ce shi ma a matsayinsa na ɗan kabilar Igbo ya taɓa fuskantar irin wannan kallon ƙyama saboda asalinsa. Ya ƙara da cewa yana jin tausayin Fulani masu bin doka da oda waɗanda ake zarginsu saboda laifukan wasu masu aikata ta’addanci da ba sa wakiltar al’ummarsu.
Ya bayyana cewa tarihi ya nuna yadda aka yi yaƙi da irin wannan wariya a wasu ƙasashe, yana mai ambaton gwagwarmayar kare haƙƙin bil’adama a Amurka da kalaman Martin Luther King Jr. na cewa ya kamata a riƙa hukunta mutum bisa halayensa ba launin fata ko asalinsa ba.
Obi ya jaddada cewa duk wanda ya aikata laifi ya kamata ya fuskanci hukunci a matsayin mutum ɗaya, ba a jingina laifinsa ga ƙabilarsa ba. A cewarsa, “ɓarawo ɓarawo ne, ɗan ta’adda ɗan ta’adda ne, mai garkuwa da mutane ma mai garkuwa da mutane ne, ba wakilan wata ƙabila ba ne.”
Ya kuma yi kira ga ‘yan Nijeriya da su rungumi haɗin kai tare da girmama bambancin al’adu da ƙabilu, yana mai cewa hakan ne zai taimaka wajen gina ƙasa mai zaman lafiya da adalci.
