DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Tuesday, July 7, 2026
HomeLabaraiƳan bindiga sun riƙe dattawa 50 da suka je yin sulhu a...

Ƴan bindiga sun riƙe dattawa 50 da suka je yin sulhu a Zamfara

Akalla tsofaffi 50 daga ƙauyen Magamin Diddi da ke gundumar Magami/Faru a ƙaramar hukumar Maradun ta jihar Zamfara sun shiga hannun ‘yan bindiga bayan sun je ganawa da wani ƙasurgumin shugaban ‘yan bindiga domin tattaunawar sulhu.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa shugaban ‘yan bindigar mai suna Jammo, wanda ke iko da dajin Natsira da ke Maradun, ne ya tsare mutanen bayan sun isa wurin ganawar. Shugaban ƙaramar hukumar Maradun, Sanusi Ahmad Dosara, ya tabbatar da faruwar lamarin, yana mai cewa mutanen sun je tattaunawar ne ba tare da amincewar gwamnati ba.

Gwamnatin jihar Zamfara ƙarƙashin Gwamna Dauda Lawal ta sha bayyana adawarta ga yin sulhu da ‘yan bindiga. Dosara ya ce duk da cewa gwamnatin na ba mazauna yankin kariyar jami’an tsaro domin zuwa kasuwa da dawowa, mutanen sun zaɓi shiga tattaunawar da Jammo da kansu.

A cewar Kansilan Magami/Faru, Bello Husseini, Jammo ya nemi a yi sulhu ne bayan wasu hare-haren jami’an tsaro da suka yi sanadin mutuwar wasu daga cikin yaransa.

Sai dai da kwamitin mutum 50 ya isa wurin ganawar, ya yaudare su tare da tsare su. Daga baya ya saki mutum 11 domin su sanar da jama’a abin da ya faru, yayin da mutum 39 ke ci gaba da zama a hannunsa.

Husseini ya ce Jammo yanzu yana neman Naira miliyan 24 domin a dawo masa da bindigogi uku da aka ƙwace daga hannun mutanensa.

Ya ƙara da cewa al’ummomin yankin da shugabanninsu na adawa da duk wani sulhu da ‘yan bindiga, suna masu kira ga gwamnati da jami’an tsaro su kai samame a dajin Natsira domin kawo ƙarshen matsalar tsaro a yankin.

Ukashatu Wakili
Ukashatu Wakilihttps://dclhausa.com
Ukashatu Wakili, Mataimakin Manajan Edita kuma Mai Kula da Shirin Koyon Sanin Makamar Aiki ne a DCL Hausa. A matsayinsa na ƙwararren ɗan jarida yana tsara ayyukan rediyo da kafafen sada zumunta, fassarar labarai, da tabbatar da sahihancin bayanai. Yana jagorantar shirin horaswa ga masu koyon aiki tare da kula da ingancin rubuce-rubuce da shirye-shiryen gidan jaridar.
RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata