DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Tuesday, July 7, 2026
HomeLabarai'Yan Nijeriya sun kashe sama da Naira 50bn wajen neman bizar Amurka

‘Yan Nijeriya sun kashe sama da Naira 50bn wajen neman bizar Amurka

Wani rahoto ya nuna cewa ‘yan Nijeriya sun kashe sama da Naira biliyan 50 wajen neman bizar shiga Amurka tsakanin shekarun 2023 zuwa 2024, duk da raguwar yawan bayar da bizar a wannan lokaci.

Kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito, rahoton Intelpoint wanda ya yi amfani da bayanan ma’aikatar harkokin wajen Amurka ya nuna cewa an ba ‘yan Nijeriya bizar shiga amurka guda 201,200 a cikin shekarun biyu.

Rahoton ya bayyana cewa da farashin dalar Amurka 185 a matsayin kudin neman biza ga kowane mutum, ‘yan Nijeriya sun kashe kusan dala miliyan 37.2, wanda ya kai kimanin Naira biliyan 50.7 bisa canjin kudi na Naira 1,360 kan dala daya.

Yawan bizar da aka bayar ya ragu da kusan kashi 23 cikin dari, inda ya sauka daga 113,900 a shekarar 2023 zuwa 87,300 a shekarar 2024.

Wannan na nufin an samu raguwar bayar da biza 26,600 a cikin shekara guda.

Bizar da aka bayar domin kasuwanci da yawon bude ido ce mafi yawan wadanda aka amince da su a shekarar 2024, inda suka kai kashi 83 cikin dari na dukkan bizar da aka bayar, yayin da aka bayar da bizar dalibai (F1) ta kai kusan kashi bakwai cikin dari.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata