Bangaren jam’iyyar PDP da Kabiru Tanimu Turaki ke jagoranta ya amince da shirin G-100 na hada kan jam’iyyun adawa domin kalubalantar jam’iyyar APC a zaben 2027.
Bangaren ya bayyana matsayinsa ne a wata sanarwa da sakataren yada labaransa na kasa, Ini Ememobong, ya fitar ranar Talata, bayan taron farko na G-100 da aka gudanar ranar Litinin a cibiyar Shehu Musa Yar’Adua da ke Abuja.
Jaridar Punch ta ruwaito taron ya hada wakilan jam’iyyun adawa domin tattauna hanyoyin hadin gwiwa da kuma yiwuwar tsayar da dan takara guda da zai fafata da dan takarar jam’iyyar APC a zaben shugaban kasa na 2027.
Bangaren PDP ya ce matakin da ya dauka na shiga shirin ya samo asali ne daga halin da ya ce ’yan Nijeriya ke ciki sakamakon tsadar rayuwa da sauran matsalolin da suke fuskanta karkashin gwamnatin Shugaba Bola Tinubu da jam’iyyar APC.
A cikin sanarwar, jam’iyyar ta ce ta amince da tsarin G-100, wato kungiyar dattawan siyasa da masu ruwa da tsaki 100 na adawa, domin samar da hadin gwiwar da zai hada jam’iyyun adawa wajen kalubalantar APC a babban zaben 2027.
Shugaban bangaren PDP na kasa, Kabiru Tanimu Turaki, ya ce shigar jam’iyyar cikin shirin ta dogara ne kan alkawarin cewa za a tafiyar da tsarin bisa gaskiya, daidaito, amfani da bayanai wajen yanke hukunci da kuma samar da dama ga kowa. Ya ce sakamakon irin wannan tsari zai iya samar wa ’yan Nijeriya ingantaccen shugabanci da zai rage talauci da matsalar rashin tsaro.
Jam’iyyar ta ce wannan matsaya ta yi daidai da matsayinta na baya na yin aiki tare da jam’iyyun siyasa da kungiyoyin da suke da burin kalubalantar APC tare da ceto kasar daga matsalolin da take fuskanta.
Ta kuma bayyana halartar taron G-100 na ranar Litinin a matsayin wata alama ta shirinta na bayar da gudunmawa wajen samar da tsarin hadin gwiwar adawa da zai karbe mulki daga jam’iyyar mai ci tare da sake gina Nijeriya domin amfanin al’umma.
A taron G-100, wanda wakilan jam’iyyun adawa shida suka halarta, an amince da fara tsarin tattaunawa na musamman kan hadin kan adawa gabanin zaben 2027. An kuma amince da kafa kwamitoci da kungiyoyin aiki domin tsara shawarwari kan hadin kan adawa, shirin gyaran kasa da kuma hanyar da za a bi wajen samar da dan takarar shugaban kasa guda.
Wannan yunkuri na zuwa ne yayin da jam’iyyun adawa ke kokarin kauce wa maimaita abin da ya faru a zaben shugaban kasa na 2023, lokacin da kuri’un adawa suka rabu tsakanin ’yan takara da suka hada da Atiku Abubakar, Peter Obi da Rabiu Kwankwaso, lamarin da ya taimaka wajen samun nasarar Bola Tinubu.
Sai dai Atiku da Obi ba su halarci taron G-100 na ranar Litinin ba. Bayan taron, sakataren yada labarai na jam’iyyar ADC na kasa, Bolaji Abdullahi, ya ce rashin halartar Atiku ba shi da wata babbar illa, domin taron ya fi mayar da hankali kan hadin kan jam’iyyun siyasa ne ba wai ’yan takarar shugaban kasa kadai ba.
