Hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta Nijeriya (EFCC) ta bukaci tsohon gwamnan jihar Bayelsa, Timipre Sylva, wanda ta ayyana a matsayin wanda ake nema ruwa a jallo, da ya mika kansa domin amsa tambayoyi kan zargin almundahana da ta shafi dala miliyan 14.86.
Jaridar Punch ta ruwaito mai magana da yawun EFCC, Dele Oyewale, ya bayyana hakan ne ranar Litinin, yayin da yake mayar da martani kan zargin da Sylva ya yi cewa hukumar ta fara gudanar da ayyukanta ne kamar wata hukuma ta jam’iyyar APC maimakon kasancewarta ta gwamnati.
Oyewale ya ce tunda hukumar ta ayyana Sylva a matsayin wanda ake nema, ya kamata ya gabatar da kansa domin bincike. Sylva ya sanar da ficewarsa daga jam’iyyar APC a ranar Litinin, inda ya ce ya aika wa EFCC kwafin wasikar murabus dinsa tare da zargin hukumar da zama tamkar wani bangare na jam’iyyar mai mulki.
A cikin wasikar murabus dinsa, Sylva ya zargi APC da yin watsi da akidun da aka kafa jam’iyyar a kansu, yayin da ya ce gwamnatin Shugaba Bola Tinubu ta gaza cika burin mafi yawan ’yan Nijeriya. Ya ce bayan tuntubar iyalansa, abokan huldarsa da sauran masu ruwa da tsaki, ya yanke shawarar barin jam’iyyar.
Tsohon gwamnan ya kuma ce ba zai ci gaba da kasancewa cikin jam’iyyar da shugabanninta, a cewarsa, suka rungumi ra’ayin cewa komai ya halatta a siyasa ba. Ya bayyana cewa akidun da aka kafa APC a kansu sun sauyi matuka, yana mai cewa hakan ya sa ya kasa ci gaba da kasancewa cikinta.
Sylva ya ce ya saka EFCC cikin wadanda aka aika wa wasikar murabus dinsa ne saboda yadda yake zargin hukumar da kara mayar da ayyukanta na siyasa. Ya kuma bayyana fargabar cewa matakin da ya dauka na ficewa daga APC na iya janyo masa karin bincike, amma ya ce a shirye yake ya dauki wannan hadarin.
EFCC ta ayyana Sylva a matsayin wanda ake nema tun watan Nuwamban 2025 bisa zargin hada baki da kuma karkatar da dala 14,859,257. Baya ga haka, an alakanta shi da wani zargin shirya makarkashiya kan gwamnatin Tinubu, inda aka sanya sunansa cikin wadanda ake kara a wata tuhuma mai tuhume-tuhume 13 da suka hada da cin amanar kasa, laifukan da suka shafi ta’addanci, hada baki da safarar kudaden haram.
Sylva ya musanta hannu a makarkashiyar, kuma zarge-zargen da ake masa suna gaban kotu, ba tare da an same shi da laifi ba. A watan Mayun 2026, Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta bayar da umarnin kwace wasu kadarori tara da ake alakanta su da shi na wucin gadi, bayan wata bukata da EFCC ta gabatar.
Tsohon gwamnan ya rike mukamin gwamnan Bayelsa daga shekarar 2007 zuwa 2012, kafin daga bisani ya zama karamin ministan albarkatun man fetur a gwamnatin tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari.
