DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Wednesday, May 13, 2026
HomeLabaraiRashin tsaro na barazana ga sahihin zaɓe a Nijeriya - INEC

Rashin tsaro na barazana ga sahihin zaɓe a Nijeriya – INEC

Shugaban Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Nijeriya (INEC), Farfesa Joash Amupitan, ya bayyana cewa matsalar rashin tsaro da ke ƙaruwa a sassan Nijeriya na iya zama babbar barazana ga gudanar da sahihin zaɓe a ƙasar.

Amupitan ya bayyana hakan ne ranar Laraba yayin wata ziyara da ya kai wa Sufeto Janar na ‘Yan Sanda, Olatunji Disu, a Abuja domin tattauna shirye-shiryen zaɓen 2027.

Daily Trust ta ruwaito cewa shugaban INEC ya ce tashe-tashen hankula, magudin zaɓe da barazanar tsaro na iya rage amincewar jama’a da tsarin zaɓe idan ba a ɗauki matakan gaggawa ba.

Ya ce, “Tsarin zaɓen Nijeriya ya fuskanci ƙalubale da dama tsawon shekaru, daga magudin zaɓe zuwa barazanar tashin hankali da sayen ƙuri’u, waɗanda ke rage amincewar masu zaɓe.”

Amupitan ya ƙara da cewa rashin tsaro a sassa daban-daban na ƙasar na barazana ga gudanar da zaɓe cikin adalci da gaskiya.

Ya buƙaci hukumomin tsaro su fara gano wuraren da ka iya fuskantar rikici tare da ɗaukar matakan kariya domin kare masu zaɓe da jami’an zaɓe.

Shugaban INEC ya kuma ambaci zaɓukan gwamna na Ekiti da Osun da za a gudanar nan gaba, da kuma zaɓukan cike gurbi a wasu jihohi, yana mai cewa za su zama gwaji ga dimokuraɗiyyar Nijeriya.

Ya ce hukumar na ƙoƙarin tabbatar da cewa ‘yan gudun hijira da masu nakasa sun samu damar kaɗa ƙuri’arsu cikin sauƙi.

A nasa ɓangaren, Sufeto Janar na ‘Yan Sanda, Olatunji Disu, ya yi alƙawarin haɗin gwiwa da INEC domin tabbatar da zaman lafiya da sahihin zaɓe a faɗin ƙasar.

Ukashatu Ibrahim Wakili
Ukashatu Ibrahim Wakilihttps://dclhausa.com
Ukashatu Wakili, Mataimakin Manajan Edita kuma Mai Kula da Shirin Koyon Sanin Makamar Aiki ne a DCL Hausa. A matsayinsa na ƙwararren ɗan jarida yana tsara ayyukan rediyo da kafafen sada zumunta, fassarar labarai, da tabbatar da sahihancin bayanai. Yana jagorantar shirin horaswa ga masu koyon aiki tare da kula da ingancin rubuce-rubuce da shirye-shiryen gidan jaridar.
RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata