DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Tuesday, July 7, 2026
HomeLabaraiSama da mutane dubu 79 aka hallaka a hare-haren ta’addanci a Nijeriya...

Sama da mutane dubu 79 aka hallaka a hare-haren ta’addanci a Nijeriya cikin shekara shida – Binciken ORFA

Wani sabon bincike da Cibiyar Observatory for Religious Freedom in Africa (ORFA) ta gudanar ya nuna cewa mutane 79,323 ne suka rasa rayukansu sakamakon hare-haren ta’addanci a Nijeriya tsakanin shekarar 2020 zuwa 2025.

Rahoton, mai taken “Four Times Boko Haram? How the World Misreads Nigeria’s Violence,” ya kuma bayyana cewa an yi garkuwa da fararen hula 34,773 a cikin wannan lokaci.

A cewar ORFA, hare-haren sun kai matsakaicin hare-hare bakwai da mutuwar mutane 36 a kowace rana, yayin da sama da mutane 42,000 daga cikin waɗanda aka yi ajali fararen hula ne.

Rahoton ya ce bayan nazarin bayanai na tsawon shekaru shida, an gano cewa ƙungiyoyin Boko Haram da ISWAP ne suka haddasa kusan kashi 12 cikin ɗari na ta’addanci a kan fararen hula, yayin da abin da rahoton ya kira ƙungiyoyin ’yan bindigar Fulani suka haddasa kusan kashi 44 cikin ɗari.

Sai dai ORFA ta jaddada cewa wannan bayanin bai shafi al’ummar Fulani baki ɗaya ba, tana mai cewa mafi yawan Fulani ba su da alaƙa da ayyukan ta’addanci.

Binciken ya kuma nuna cewa an yi garkuwa da fararen hula 34,773, inda ƙungiyoyin da aka danganta da Fulani suka aikata kashi 43 cikin ɗari na sace-sacen, yayin da wasu ƙungiyoyin da ba a tantance ba suka aikata kashi 49 cikin ɗari.

Rahoton ya ƙara da cewa Kiristoci 28,551 ne aka hallaka cikin wannan lokaci, yayin da Musulmi 13,224 suka rasa rayukansu. Haka kuma ya yi iƙirarin cewa Kiristocin da aka yi garkuwa da su na fuskantar biyan kuɗin fansa mai yawa, tsawaita tattaunawar fansa da kuma barazanar kisa fiye da Musulmai.

Ƙungiyar ORFA ta ce ta tattara bayananta ne ta hanyar haɗa bayanai daga binciken da ta gudanar kai tsaye, abokan hulɗarta, cibiyoyin bincike, kafafen yaɗa labarai, ƙungiyoyi masu zaman kansu da kuma bayanan kafafen sada zumunta da aka tantance.

A ƙarshe, ƙungiyar ta yi kira da a yi la’akari da dukkan bangarorin da ke haddasa rikicin domin samun mafita mai ɗorewa ga matsalar tsaro da ke addabar Nijeriya.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata