Gwamnan Jihar Kaduna, Uba Sani, ya ce Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya fi duk wani shugaban Nijeriya da ya gabata gudanar da ayyukan ci gaba a Arewacin ƙasar, musamman ta fannin ababen more rayuwa, noma da kiwon lafiya.
Sani ya bayyana hakan ne yayin wata hira da ya yi da gidan talabijin na ARISE, inda ya ce yana magana ne bisa hujjoji da alkaluma, ba ra’ayi kawai ba.
A cewarsa, babu wani shugaban ƙasa da ya aiwatar da ayyukan ci gaba a Arewa irin waɗanda gwamnatin Tinubu ta yi cikin shekaru uku da suka gabata.
Gwamnan ya kuma yi watsi da ra’ayin cewa Arewa ba za ta goyi bayan sake zaɓen Tinubu a 2027 ba, yana mai cewa shugaban zai samu ƙuri’u fiye da waɗanda ya samu a zaɓen 2023.
Ya danganta hakan da ayyukan raya ƙasa da gwamnatin tarayya ke aiwatarwa a Kaduna da sauran jihohin Arewa.
Daga cikin ayyukan da ya lissafa akwai titin Abuja zuwa Kaduna, wanda ya ce gwamnati ta biya sama da naira biliyan 600 domin kammala shi kafin watan Nuwamba na wannan shekara.
Ya kuma ambaci titin Kaduna zuwa Birnin Gwari da aka ware wa naira biliyan 178 bayan shafe fiye da shekara 25 ba a kammala shi ba.
Sani ya ƙara da cewa gwamnatin Tinubu ta tallafa wa jihohi a fannin noma, tare da samar da takin zamani ga manoma, abin da ya taimaka wa Kaduna wajen zama kan gaba a shirin Special Agro-Industrial Processing Zones (SAPZ).
Haka kuma ya yabawa gwamnatin tarayya kan amincewa da kafa Jami’ar Kimiyya da Fasaha a Kudancin Kaduna, mayar da wani asibiti zuwa Cibiyar Kiwon Lafiya ta Tarayya, da kuma amincewa da aikin jirgin ƙasa na cikin birnin Kaduna da kudinsa ya kai naira tiriliyan ɗaya.
Gwamnan ya ce waɗannan ayyuka suna nuna ƙudirin gwamnatin Tinubu na inganta rayuwar al’umma da bunƙasa ci gaban Arewacin Nijeriya.
