DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Monday, September 14, 2026
HomeLabaraiShayar da jarirai ba ta sa nonon mace ya zube, in ji...

Shayar da jarirai ba ta sa nonon mace ya zube, in ji masana kiwon lafiya

Masana kiwon lafiya sun gargaɗi iyaye mata da su daina ƙin shayar da jariransu saboda kuskuren fahimtar cewa shayarwa ce ke sa nono ya zube.

Sun bayyana cewa zubewar nono abu ne da ke faruwa a dabi’ance na rayuwar ɗan adam, yayin da mace ke ƙara shekaru, ba saboda shayar da jariri ba.

Jaridar Punch ta ruwaito cewa an bayyana hakan ne a yayin ƙaddamar da bikin makon shayar da nono ta Duniya na shekarar 2026 da aka gudanar a jihar Bauchi.

Da yake jawabi a wajen taron manema labarai, shugaban hukumar kula da lafiya a matakin farko ta jihar Bauchi, Dakta Rilwanu Mohammed, ya nuna damuwarsa kan yadda wasu iyaye mata ke hana jariransu nono saboda suna ganin hakan zai sa nononsu ya zube kuma su tsufa da wuri.

Ya ce irin wannan kuskuren fahimta na jefa yara cikin haɗarin rashin abinci mai gina jiki da kuma kamuwa da cututtuka, musamman idan ba a ba su nonon uwa kaɗai cikin watanni shida na farkon rayuwar su ba.

Dakta Mohammed ya ce, “Ba shayar da jariri ba ne ke sa nono ya zube, nono zai zube da shekaru ko mace ta shayar da jariranta ko ba ta shayar ba.” ya ƙara da cewa shayar da jariri da nonon uwa kaɗai na daga cikin hanyoyin da suka fi tasiri wajen kare yara daga rashin lafiya da rashin abinci mai gina jiki.

A nata jawabin, shugabar ofishin UNICEF na Bauchi, Dakta Nuzhat Rafique, ta bayyana cewa shayar da jarirai na ceton rayuka, tare da ƙarfafa iyaye mata su rungumi ingantattun hanyoyin shayarwa domin tabbatar da lafiyar ƴaƴansu.

Ta ce taken makon shayar da nono na Duniya na bana mai taken “Breastfeeding for a Sustainable Start in Life: Strengthen What Works” na nuni da muhimmancin ci gaba da aiwatar da hanyoyin da aka tabbatar suna inganta lafiyar yara da abincinsu.

Rafique ta yabawa Gwamnatin jihar Bauchi bisa amincewa da hutun haihuwa na watanni shida tare da cikakken albashi ga ma’aikata mata, tana mai cewa hakan zai ba iyaye mata damar shayar da jariransu yadda ya kamata.

Haka kuma ta yaba da ware Naira miliyan 500 a matsayin gudunmawar gwamnatin jihar ga asusun ciyar da yara, tana mai fatan za a gaggauta fitar da kuɗin domin sayen kayan tallafa wa abinci mai gina jiki.

A cewarta, duk da cewa sama da kashi 90 cikin 100 na iyaye mata a Bauchi na shayar da ƴaƴansu, har yanzu bin ƙa’idojin shayarwa yadda ya kamata bai kai matakin da ake buƙata ba.

Ta bayyana cewa kashi 12 cikin 100 ne kawai na jarirai ke fara shan nono cikin awa ta farko bayan haihuwa, yayin da kashi 26 cikin 100 ne kawai ke samun nonon uwa kaɗai har tsawon watanni shida na farko.

Ta kuma bayyana cewa ya kamata a fara ba jariri nono cikin awa ta farko bayan haihuwa, musamman madarar farko (colostrum), wadda ta bayyana a matsayin rigakafin farko da jariri ke samu saboda ƙarfafa garkuwar jikinsa.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata