DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Tuesday, September 15, 2026
HomeSiyasaSheikh Jingir mutumin kirki ne da ke kokarin samar da haɗin kan...

Sheikh Jingir mutumin kirki ne da ke kokarin samar da haɗin kan kasa – Gwamnan Kano

Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, tare da takwarorinsa na jihohin Yobe, Sokoto da Jigawa, sun yabawa shugaban majalisar malamai ta Jama’atu Izalatil Bid’ah Wa Iqamatus Sunnah (JIBWIS), Sheikh Muhammad Sani Yahaya Jingir, bisa gudunmawar da yake bayarwa wajen inganta haɗin kai, zaman lafiya da fahimtar juna tsakanin musulmi da sauran ’yan Nijeriya.

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da kakakin gwamnan Kano, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar a ranar Lahadi, bayan wani taron karawa juna sani na kasa da aka gudanar na yini guda a Saddiqa Event Centre da ke Jos, jihar Plateau, mai taken inganta shiga harkokin siyasa da goyon bayan adalci domin samar da haɗin kai da ci gaban Nijeriya.

A yayin taron, JIBWIS ta bukaci mambobinta a fadin kasar nan su mara wa shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu da mataimakinsa, Kashim Shettima, baya tare da kada musu kuri’a a zaben shugaban kasa na shekarar 2027.

Shugaban gudanarwa na kasa na JIBWIS, sheikh Abdulnasir Abdulmuhuyi, ya bayyana cikakken amincewarsa da gwamnatin Tinubu da Shettima, yana mai cewa Gwamnatin Nijeriya ta nuna rikon amana da jajircewa wajen ci gaban kasa cikin shekaru ukun farko na mulkinta, don haka ya ce gwamnatin ta cancanci samun karin wa’adi domin ci gaba da ayyukan ci gaba ga ƙasar.

Shi ma shugaban majalisar malamai ta JIBWIS, sheikh Muhammad Sani Yahaya Jingir, ya yi kira ga mambobin kungiyar a duk fadin Nijeriya da su sabunta goyon bayansu ga Tinubu da Shettima a zaben 2027.

A nasa bangaren, gwamnan Yobe, Mai Mala Buni, wanda ya yi magana a madadin gwamnonin hudu, ya yabawa sheikh Jingir kan jajircewarsa wajen amfani da wa’azi domin karfafa haɗin kan kasa da zaman lafiya.

Mataimakin shugaban majalisar dattawa, sanata Barau I. Jibrin, ya ce ’yan Nijeriya ba za su iya sake su rasa gwamnatin Tinubu da Shettima a 2027 ba, yayin da ya kuma yabawa sheikh Jingir kan kokarinsa na tabbatar da haɗin kai da zaman lafiya.

Shima a nasa ɓangaren, Hon. Ibrahim Kabir Masari da gwamna Mai Mala Buni sun bayar da tallafin naira miliyan 300 kowannensu domin kafa Fortune University, wadda sheikh Jingir ya assasa.

Taron ya samu halartar fitattun malaman addini, shugabannin siyasa, jami’an gwamnati da mambobin JIBWIS daga sassa daban-daban na Nijeriya, inda suka tattauna kan muhimmancin shiga harkokin siyasa, tabbatar da adalci, ƙarfafa haɗin kan kasa da kuma dorewar ci gaba.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata