DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Wednesday, May 13, 2026
HomeKetareShugaban mulkin sojin Mali ya karɓi mukamin ministan tsaro

Shugaban mulkin sojin Mali ya karɓi mukamin ministan tsaro

Shugaban mulkin sojin Mali, Assimi Goita, ya karɓi ƙarin muƙamin ministan tsaro bayan rasuwar wanda ke riƙe da kujerar, sakamakon hare-haren ta’addanci da suka girgiza ƙasar.

TRT Afrika ta rawaito cewa an sanar da wannan mataki ne a wata doka da aka karanta a gidan talabijin na ƙasar a ranar Litinin, bayan mutuwar tsohon ministan.

Bayanai sun nuna cewa tsohon ministan, Sadio Camara, ya rasu ne sakamakon harin bam da aka kai masa a gidansa, yayin da hare-haren suka addabi wurare daban-daban a ƙasar.

Hare-haren dai sun haɗa da farmaki kan sansanonin sojoji da wasu muhimman wurare, inda mayaƙan ‘yan aware na Tuareg da kuma masu alaƙa da ƙungiyar Al-Qaeda suka kai hare-haren.

Rahotanni sun nuna cewa wannan farmaki shi ne mafi girma da aka gani a Mali cikin kusan shekaru 15, lamarin da ya jefa ƙasar cikin mawuyacin hali na tsaro.

A sakamakon hare-haren, akalla mutum 23 ne suka rasa rayukansu, yayin da da dama suka jikkata a wurare daban-daban, ciki har da yankunan da ke kusa da babban birnin ƙasar, Bamako.

Hukumar kula da yara ta Majalisar Ɗinkin Duniya, wato UNICEF, ta bayyana cewa fararen hula da yara na cikin waɗanda suka mutu ko suka jikkata sakamakon rikicin.

Matakin da Shugaba Goita ya ɗauka na riƙe kujerar Ministan Tsaro na zuwa ne a wani yunƙuri na ƙarfafa tsaro da daidaita harkokin soja a ƙasar da ke fama da rikici.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata