Gwamnatin Jihar Katsina ta tabbatar da cewa sojojin rundunar 17 Brigade sun kashe wasu ‘yan ta’adda huɗu ciki har da jagora Bishir Holami, tare da kwato makamai da wasu kayayyaki a hanyar Turare–Yantumaki.
Wannan na kunshe ne cikin wata sanarwa da Kwamishinan Tsaro na Cikin Gida, Dokta Nasir Mu’azu ya fitar ranar 2 ga Mayu, 2026, inda ya ce lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 11:40 na safe bayan da ‘yan bindiga suka kai hari ga sojojin.
Sanarwar ta ce sojojin sun mayar da martani cikin gaggawa, suka bi maharan har suka kashe su ba tare da samun asara a ɓangarensu ba.
An ce daga cikin kayan da aka kwato akwai bindiga kirar AK-47 guda ɗaya da alburusai, babura biyu, wayoyi guda bakwai ciki har da na Android, da kuɗi naira 153,400.
Binciken farko ya nuna cewa waɗanda aka kashe sun haɗa da Bishir Holami, Jamilu Baki, Ibrahim Doro da Abdurraman Maje, waɗanda ake zargi da kai hare-hare a yankunan Gobirawa, Raddawa, Kuki da wasu sassan ƙananan hukumomin Dutsinma da Matazu.
Gwamnatin jihar ta ce kashe waɗannan mutane babbar nasara ce a yaƙi da ‘yan bindiga, musamman ga wani jagoran su Muhammadu Fulani da ke addabar yankunan Matazu, Musawa, Charanchi da Kankia.
Ta kuma jaddada cewa gwamnatin Gwamna Dikko Umaru Radda ba za ta huta ba har sai an kawar da matsalar tsaro a jihar baki ɗaya.
