Ministan Kuɗi kuma mai kula da tattalin arzikin Nijeriya, Taiwo Oyedele, ya ce gwamnatin tarayya ba za ta dawo da tsarin tallafi ko saka farashin kayayyaki ba, yana mai jaddada cewa za ta ci gaba da bin tsarin tattalin arziki na kasuwa.
Kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito, Oyedele ya bayyana hakan ne a wani taro da aka gudanar a birnin Paris bayan ganawa da masu zuba jari na duniya ranar Talata.
Ministan ya ce gwamnati na son kauce wa manufofin da ke kawo tangarda ga tattalin arziki, tare da tabbatar da cewa akwai tsauraran dokoki da za su hana ‘yan kasuwa anfani da jama’a.
Ya ce, “Ba za mu dawo da tallafi ba, kuma ba za mu saka farashin kayayyaki ba saboda mun yi imani da tsarin kasuwa. Amma za mu tabbatar da cewa dokoki sun hana masu kaya da masana’antu zalintar ‘yan Nijeriya.”
Oyedele ya ce gwamnati na aiki ne domin samar da tsarin da kasuwa za ta rika kayyade farashi, amma cikin adalci da kariya ga jama’a.
Ya kuma yi magana kan rikicin Iran, yana mai cewa duk da cewa matsalar abin takaici ce, amma ta buɗe damammaki ga Nijeriya musamman a bangaren makamashi da zuba jari.
A cewarsa, Nijeriya na ƙoƙarin anfani da sauye-sauyen tattalin arzikin duniya wajen tara kuɗaɗen shiga da kuma amfani da su wajen rage hauhawar farashi da bunƙasa tattalin arziki.
Ministan ya nuna kwarin gwiwa kan makomar tattalin arzikin ƙasar, yana mai cewa “akwai kwanaki masu kyau a gaban Nijeriya.”
