Shugaban Nijeriya, Bola Ahmed Tinubu, ya umarci a karkatar da kudaden da hukumar EFCC mai yaƙi da cin hanci da rashawa a Nijeriya ta kwato zuwa ssusun ba da lamunin karatun ɗalibai na Nijeriya (NELFUND), domin ƙarfafa asusun da kuma biyan buƙatun ɗalibai da ke ƙaruwa.
Ministan Ilimi, Dakta Tunji Alausa, ne ya bayyana hakan a ranar Laraba yayin da yake yi wa manema labarai bayani bayan taron majalisar zartarwa ta tarayya (FEC).
Ministan ya ce majalisar zartarwar ta amince da umurnin Shugaba Tinubu na karkatar da dukkan ribar hannun jarin ta Capital Market Trust Fund da Dormant Account Trust Fund zuwa NELFUND.
Ya ce matakin zai taimaka wajen samar da isassun kudade ga NELFUND domin ci gaba da gudanar da shirin bayar da lamunin karatu ga ɗaliban Nijeriya.
Dakta Alausa ya bayyana cewa umurnin shugaban kasa ya shafi kudaden da EFCC ta kwato kuma suke hannun hukumar a matsayin tsabar kuɗi da ba su da wata takaddamar shari’a, ba tare da karkatar da kadarorin da aka ƙwace ko kudaden da ke ƙarƙashin shari’a ba.
A cewarsa, Shugaba Tinubu ya ɗauki matakin ne domin tabbatar da cewa NELFUND na da isasshen ƙarfin kuɗi da zai ba shi damar cika nauyin da ke kansa wajen tallafa wa ɗaliban manyan makarantun Nijeriya.
Ministan ya ce wannan mataki ya yi daidai da alkawarin da Shugaba Tinubu ya yi na tabbatar da cewa ɗaliban Nijeriya sun samu damar ci gaba da karatunsu ba tare da matsalar rashin kuɗin makaranta ta zama babban cikas ba.
Ya ƙara da cewa kudaden da za a karkatar zuwa NELFUND za su haɗa da dukkan kudaden EFCC da aka kwato waɗanda ba sa ƙarƙashin wata takaddamar shari’a.
Wannan mataki na zuwa ne a daidai lokacin da yawan ɗaliban da ke neman tallafin NELFUND ke ƙaruwa, lamarin da ya sa ake buƙatar ƙarin hanyoyin samar da kuɗaɗen gudanar da shirin.
Tinubu ya bayyana cewa manufar karkatar da waɗannan kudade ita ce ƙarfafa NELFUND domin ci gaba da biyan buƙatun ɗaliban Nijeriya tare da tabbatar da dorewar shirin lamunin karatu.
