DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Monday, September 14, 2026
HomeLabaraiINEC ta miƙa wa Adeleke takardar shaidar lashe zaɓen Osun

INEC ta miƙa wa Adeleke takardar shaidar lashe zaɓen Osun

Hukumar zaɓen Nijeriya INEC ta miƙa wa Gwamnan jihar Osun, Ademola Nurudeen Jackson Adeleke, takardar shaidar lashe zaɓen gwamnan jihar da aka gudanar a ranar 15 ga Agusta, 2026.

An miƙa takardar shaidar ga Adeleke ne a hedikwatar INEC da ke Osogbo da misalin ƙarfe 1:30 na rana ranar Laraba, yayin da mataimakin Gwamnan jihar, Prince Kola Adewusi, shi ma ya karɓi tasa.

Adeleke, wanda ya tsaya takara a ƙarƙashin jam’iyyar Accord, ya samu ƙuri’u 511,067, inda ya kayar da babban abokin hamayyarsa na jam’iyyar APC, Munirudeen Bola Oyebamiji, wanda ya samu ƙuri’u 444,815.

Hakan ya ba Adeleke tazarar ƙuri’u 66,252, yayin da ɗan takarar jam’iyyar ADC, Najeem Salaam, ya zo na uku da ƙuri’u 17,180.

Adeleke ya samu nasara a ƙananan hukumomi 19 daga cikin 30 na jihar, yayin da Oyebamiji ya lashe sauran ƙananan hukumomi 11.

Da take jawabi yayin miƙa takardun shaidar, Kwamishiniyar INEC ta Jihar Osun, Mrs Oluwatoyin Babalola, ta ce an gudanar hakan ne bisa tanadin dokokin hukumar, tare da tabbatar da cewa takardun sun nuna sahihin ikon da masu zaɓe suka ba Adeleke da Adewusi.

Ta kuma yaba wa hukumomin tsaro, ƙungiyoyin fararen hula, kafafen yaɗa labarai da sarakunan gargajiya bisa gudummawar da suka bayar wajen ganin an gudanar da zaɓen.

Babalola ta bayyana yawan waɗanda suka fito suka kaɗa ƙuri’a da kashi 43.2, inda ta taya Adeleke murna tare da roƙonsa ya kasance mai sassaucin ra’ayi da afuwa bayan nasarar da ya samu.

Shi ma Kwamishinan INEC na Kasa mai kula da Jihar Osun, Farfesa Kunle Ajayi, ya bayyana bikin a matsayin muhimmin mataki ga dimokuraɗiyya da al’ummar jihar.

Ya yaba wa masu zaɓe bisa fitowa suka yi amfani da ‘yancinsu duk da wasu tashe-tashen hankula da suka faru kafin zaɓen, yana mai cewa INEC ta je Osun ne domin kare ƙa’idojin dimokuraɗiyya, ba domin goyon bayan wani ɗan takara ba.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata