Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya sake jaddada aniyar gwamnatinsa na ƙara ƙaimi wajen yaƙi da matsalar tsaro tare da tabbatar da ceto duk mutanen da ke hannun masu garkuwa da mutane da sauran masu aikata laifuka a faɗin Nijeriya.
Kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito, Shugaban ya bayyana hakan ne ta bakin Sakataren Gwamnatin Tarayya, Sanata George Akume, a wajen taron addu’ar mabiya addinin Kirista da aka gudanar a Cibiyar Kiristoci ta Ƙasa da ke Abuja a wani ɓangare na bukukuwan Ranar Dimokuraɗiyya ta 2026.
Tinubu ya ce gwamnatin Nijeriya ba za ta taɓa mika wuya ga ta’addanci, fashi da makami ko duk wani nau’in tsoratarwa daga masu aikata laifuka ba. Ya ce kare rayuka da dukiyoyin al’umma na daga cikin manyan abubuwan da gwamnatinsa ta sa a gaba.
Ya amince cewa hare-hare da sace-sacen mutane da ake ci gaba da samu a wasu sassan ƙasar na nuna akwai sauran aiki a gaba, amma ya tabbatar da cewa gwamnati na tallafa wa hukumomin tsaro da kayan aiki da sauran abubuwan da suke buƙata domin kare al’umma da kuma mutuncin ƙasar.
Shugaban ya kuma ce gwamnati na sane da ƙalubalen tsadar rayuwa, matsalar tsaro, sace-sacen mutane da kuma raba mutane da muhallansu da ke addabar wasu yankuna. Ya ce gwamnati ta ji koken jama’a kuma tana aiki domin rage waɗannan matsaloli tare da ƙara isar da romon dimokuraɗiyya ga ‘yan ƙasa.
Yayin da ake tunkarar babban zaɓen 2027, Tinubu ya yi kira ga ‘yan Nijeriya su guji tashin hankali, kalaman ƙiyayya da siyasar rarrabuwar kawuna. Haka kuma ya gargadi matasa da kada su bari a yi amfani da su wajen daba, yaɗa bayanan ƙarya ko tayar da rikicin siyasa.
Ya kuma yabawa jami’an tsaro da rundunar sojin Nijeriya kan ƙoƙarin da suke yi wajen kare ƙasa da tabbatar da zaman lafiya, tare da kira ga ‘yan ƙasa su girmama sadaukarwar jaruman gwagwarmayar ranar 12 ga Yuni ta hanyar gina ƙasa mai zaman lafiya da adalci.
