Florentino Pérez ya sake zama shugaban ƙungiyar Real Madrid bayan ya yi nasara a zaɓen shugabancin ƙungiyar da aka yi karo na farko cikin shekaru 20 da aka samu ɗan takara mai hamayya da shi.
Rahotanni sun nuna cewa Pérez ya samu kuri’u 21,741 daidai da kashi 65 cikin 100, yayin da abokin hamayyarsa Enrique Riquelme ya samu kuri’u 11,814, wanda ya kai kashi 35 cikin 100 na yawan kuri’un da aka kaɗa.
Gidan talabijin na TVC ya ruwaito cewa Pérez mai shekaru 79 ya bayyana nasarar a matsayin ɗaya daga cikin manyan nasarorin zaɓe a tarihin ƙungiyar. Ya yi alƙawarin ci gaba da gina tarihin Real Madrid tare da ƙarfafa nasarorin da ƙungiyar ke samu a gida da nahiyar Turai.
Zaɓen ya biyo bayan kamfen na makonni biyu da Pérez da kansa ya ƙaddamar domin neman sabon amincewa daga mambobin ƙungiyar bayan kakar wasanni biyu da Real Madrid ta shafe ba tare da lashe babban kofi ba.
Wannan ne karo na farko tun shekarar 2006 da Pérez ya fuskanci ɗan takara a zaɓen shugabancin Real Madrid. A baya an zaɓe shi ba tare da hamayya ba a shekarun 2009, 2013, 2017, 2021 da 2025.
A lokacin jagorancinsa, Real Madrid ta lashe kofunan UEFA Champions League guda bakwai da kuma La Liga guda bakwai, abin da ya ƙara tabbatar da matsayin ƙungiyar a matsayin ɗaya daga cikin manyan ƙungiyoyin ƙwallon ƙafa a duniya.
Bayan sake cin zaɓen, Pérez ya bayyana shirinsa na dawo da José Mourinho a matsayin koci, tare da yunƙurin sayen fitattun ‘yan wasa kamar Ibrahima Konaté da Denzel Dumfries. Haka kuma ya yi nuni da yiwuwar kashe sama da Yuro miliyan 150 wajen sayen wani fitaccen ɗan wasan gaba domin ƙarfafa ƙungiyar.
A nasa ɓangaren, Enrique Riquelme ya amince da sakamakon zaɓen. Ya yi kamfen da shirin kawo Jürgen Klopp a matsayin koci da kuma sayen fitattun ‘yan wasa irin su Erling Haaland da Rodri.
