Fitaccen mawakin Afrobeats daga Nijeriya David Adeleke, wanda aka fi sani da Davido, ya ce shugaban Amurka, Donald Trump, shi ma shugaban ƙasarsa ne, saboda yana da shaidar zama ɗan ƙasar Amurka.
Jaridar Punch ta ruwaito cewa Davido ya bayyana hakan ne a ranar Talata yayin da yake mayar da martani ga wasu masu amfani da shafin X da suka soke shi kan wasikar da ya aike wa Trump dangane da zaɓen gwamnan Osun da za a gudanar ranar 15 ga Agusta.
A baya Davido ya roƙi Trump da ƙasashen duniya su sanya ido kan zaɓen, yana mai bayyana fargabar yiwuwar tashin hankali, tsoratar da masu kaɗa ƙuri’a da kuma kawo cikas ga tsarin zaɓe.
Wannan kira nasa ya jawo ce-ce-ku-ce a shafukan sada zumunta, inda wasu suka goyi bayansa yayin da wasu ke tambayar dalilin da ya sa ya nemi tsoma bakin shugaban Amurka.
Wani mai amfani da shafin X mai suna Ifedayo, wanda aka fi sani da JIMCRUZ, ya yi wa Davido ba’a tare da tambayar lafiyar kwakwalwarsa.
Davido ya mayar masa da cewa: “To ba zan iya wallafa wa shugaban ƙasata saƙo ba?”
Kazalika shima wani mai amfani da X ɗin da ake kira, ÌKÀ NATION, ya wallafa hoton Davido tare da shugaban Nijeriya, Bola Ahmed Tinubu, yana tambayar sa idan Trump ne shugaban ƙasarsa, to wane ne Tinubu?
A nan ma Davido ya amsa masa cewa Tinubu ma shugaban ƙasarsa ne, yana mai cewa yana da ‘Dual Citizenship’, wato shaidar iznin zama ɗan ƙasar Nijeriya da Amurka.
Davido, wanda asalinsa ɗan ƙasar Nijeriya da Amurka ne, ɗan’uwan Gwamnan Osun, Ademola Adeleke, ne. Ya kuma fito fili yana goyon bayan ƙoƙarin kawunsa na sake neman kujerar gwamnan jihar a karo na biyu
A cikin saƙon da ya wallafa a baya, Davido ya roƙi Trump da ƙasashen duniya su sanya ido kan halin da ake ciki a Osun, tare da kira ga ‘yan siyasa da mazauna jihar da su guji tashin hankali domin a gudanar da zaɓe cikin lumana, gaskiya da adalci.
