DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Tuesday, July 7, 2026
HomeLabaraiTrump ya ba kamfanonin tsaro umurnin kera sabbin makaman yaƙi

Trump ya ba kamfanonin tsaro umurnin kera sabbin makaman yaƙi

Shugaban Amurka, Donald Trump, ya tilasta wa kamfanonin tsaro ƙara yawan ƙera makamai, bayan yaƙin da aka yi da Iran ya rage yawan makaman da ke cikin rumbunan ajiyar sojojin Amurka.

A cikin wata takarda da ya sanya wa hannu a makon da ya gabata, Trump ya bayyana cewa akwai wasu yanayi da za su iya zama barazana ga tsaron ƙasar Amurka da shirye-shiryen kare ƙasa.

Takardar ta nuna cewa masana’antar kera makamai ta Amurka na fuskantar matsaloli da suka haɗa da ƙarancin ƙarfin samarwa, matsalolin hanyoyin samar da kayayyaki, jinkirin samar da wasu muhimman kayan aiki da kuma cikas a harkar samar da makamai.

An aika da wannan umarni ga Sakataren tsaro na Amurka, Pete Hegseth, domin tabbatar da cewa kamfanonin tsaro sun ƙara samar da makamai, rokoki da sauran kayan aikin soji da ake buƙata.

Rahotanni sun nuna cewa gwamnatin Trump na nuna damuwa kan raguwar makaman da Pentagon ke da su, musamman bayan yaƙin Iran da kuma taimakon makamai da Amurka ta bai wa Isra’ila da Ukraine a rikice-rikicen da suke fuskanta.

Masana harkokin tsaro sun bayyana cewa Pentagon ta daɗe ta na nuna damuwa kan yadda masana’antar tsaron Amurka ke jinkirin samar da makamai cikin gaggawa idan buƙata ta taso, kuma yaƙin Iran ya ƙara bayyana wannan matsala.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata