DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Monday, September 14, 2026
HomeLabaraiTun da na zama Gwamna, ban ciwo bashin ko sisin kwabo ba...

Tun da na zama Gwamna, ban ciwo bashin ko sisin kwabo ba — Uba Sani

Gwamnan jihar Kaduna, Uba Sani, ya ce tun bayan da ya karɓi mulkin jihar, gwamnatinsa ba ta ciwo wani sabon bashi ko da na sisin kwabo ba, duk da cewa tana ci gaba da biyan basussukan da gwamnatocin da suka gabata suka gada.

Gwamna Uba Sani ya bayyana hakan ne yayin wata hira da aka yi da shi a gidan talabijin na Channels ranar Alhamis, inda ya yi magana kan yadda gwamnatinsa ke gudanar da harkokin kuɗin jihar da kuma ƙarin kuɗaɗen shigar da take samu.

A cewar gwamnan, a halin yanzu jihar Kaduna na kashe kusan Naira biliyan 6.7 a duk wata wajen biyan basussukan da aka gada daga gwamnatocin baya.

Ya ce dalilin da ya sa gwamnatinsa ba ta ciwo sabon bashi ba shi ne yadda take gudanar da kuɗaɗen jihar cikin taka-tsantsan tare da fifita muhimman abubuwan da ya kamata a kashe kuɗi a kansu.

“Tun da na zama gwamna, ban ciwo bashi ko da sisin kwabo ba,” in ji Uba Sani.

Ya bayyana cewa gudanar da kuɗi cikin hikima na buƙatar zaɓar wuraren da za a fi mayar da hankali wajen zuba kuɗaɗen gwamnati, domin tabbatar da cewa an samu sakamako mai amfani ga al’umma.

Gwamnan ya kuma bayyana gwamnatinsa a matsayin mai samun nasara, inda ya ambaci noma, ilimi, samar da ababen more rayuwa, koyar da sana’o’i da tsaro a matsayin wasu daga cikin fannonin da aka samu ci gaba.

A fannin ilimi kuwa, Uba Sani ya ce gwamnatin Kaduna ta gano kusan yara 550,000 da ba sa zuwa makaranta, bayan gudanar da wani bincike na musamman ta hanyar tattara bayanan gidaje a faɗin jihar.

Ya ce zuwa yanzu an mayar da sama da yara 300,000 makaranta, yana mai cewa shirin na ci gaba da gudana domin rage yawan yaran da ba sa zuwa makaranta a jihar.

Gwamnan ya ce amfani da ingantattun bayanai wajen gano yaran na taimaka wa gwamnati wajen sanin wuraren da matsalar ta fi yawa da kuma yadda za a fi kai musu tallafin ilimi.

A ƙarshe, Uba Sani ya ce gwamnatinsa za ta ci gaba da mai da hankali kan gudanar da kuɗaɗen jihar cikin tsari, tare da tabbatar da cewa ana amfani da su wajen ayyukan da za su amfani al’ummar Kaduna.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata