Kungiyar APC ta shiyyar Arewa ta tsakiyar Nijeriya ta bai wa shugaban jam’iyyar na ƙasa, Farfesa Nentawe Yilwatda, wa’adin makonni biyu ya yi murabus bisa zargin da ta yi masa na mayar da zaɓen fidda gwani zuwa hanyar tatsar kuɗi da kuma sauya sakamakon zaɓe domin fifita wasu ‘yan takara.
Kungiyar ta bayyana hakan ne cikin wata sanarwa da shugaban ta na ƙasa, Alhaji Saleh Zazzaga, ya fitar ranar Juma’a, inda ta dora alhakin rikice-rikicen da suka biyo bayan zaɓukan fidda gwani kan kwamitin gudanarwa na jam’iyyar APC ƙarƙashin jagorancin Yilwatda.
A cewar kungiyar, an samu rahotannin cewa wasu ‘yan jam’iyyar sun sauya sakamakon zaɓe domin bai wa waɗanda suke kusa da shugabannin APC nasara, yayin da aka hana wasu ‘yan takara da ake ganin za su yi nasara shiga takara tun daga matakin tantancewa.
Kungiyar ta ce tun kafin kammala zaɓukan fidda gwani ta yi gargadi kan yadda ake gudanar da tsarin cikin rashin gaskiya, inda ta yi zargin cewa an mayar da tsarin zuwa kasuwanci da tara kuɗi daga hannun masu neman takara.
Ta kuma bayyana cewa sama da kashi 50 cikin 100 na ‘ya’yan APC a faɗin ƙasar nan ba su gamsu da yadda aka gudanar da zaɓukan fidda gwani na ‘yan majalisar jihohi, na tarayya, gwamnoni da kuma shugaban ƙasa ba.
Kungiyar APC ta Arewa ta tsakiyar ta yi zargin cewa shugaban jam’iyyar da wasu daga cikin kwamitinsa sun yi amfani da mukamansu wajen yin tasiri kan sakamakon zaɓe a jihohi daban-daban, lamarin da ta ce ya sa aka samu koke-koke da ficewar wasu manyan jiga-jigan jam’iyyar.
A cikin sanarwar, kungiyar ta yi nuni da sakamakon zaɓen fidda gwani na shugaban ƙasa inda aka bayyana cewa Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya samu ƙuri’u sama da miliyan 10, duk da cewa bayanan rajistar jam’iyyar sun nuna APC na da mambobi kusan miliyan takwas kacal.
Kungiyar ta ce wannan bambanci na adadin ƙuri’u ya nuna cewa ba zaɓe aka gudanar ba, illa dai tsarin zaɓar ‘yan takara kawai aka yi, wanda hakan ya saba wa dokokin jam’iyyar da ƙa’idojin zaɓen fidda gwani.
Har ila yau, kungiyar ta yi nuni da ficewar wasu jiga-jigan APC daga jam’iyyar zuwa wasu jam’iyyu saboda abin da suka kira rashin adalci.
Ta ambaci tsohon mataimakin shugaban majalisar dattawa, Ovie Omo-Agege, da tsohon shugaban ma’aikatan shugaban APC na ƙasa, Mustapha Bala Dawaki, a matsayin waɗanda suka fice daga jam’iyyar bayan zaɓukan fidda gwani.
A ƙarshe, kungiyar ta yi barazanar gurfanar da shugaban APC na ƙasa a kotu idan har bai yi murabus kafin ranar 12 ga watan Yuni ba, tana mai cewa za ta gabatar da hujjoji kan zargin maguɗi, tatsar kuɗi da kuma karya ƙa’idojin jam’iyyar a lokacin zaɓukan fidda gwani.
