Hukumar gudanarwar birnin tarayyar Abuja FCTA, ta gargadi masu otal-otal, wuraren taro da sauran gine-gine da su guji bai wa haramtattun kungiyoyi siyasa damar amfani da wurarensu.
Hukumar ta ce duk wani fili da aka bayar a Abuja an yi hakan ne domin gudanar da halastattun ayyuka kawai, tana mai gargadin cewa za ta kwace takardun mallakar duk wani otal ko wurin taro da aka samu yana bai wa haramtattun kungiyoyi masauki ko damar gudanar da taro.
Wannan na kunshe ne cikin wata sanarwa da mai taimaka wa ministan Abuja kan harkokin yada labarai, Mista Lere Olayinka, ya fitar ranar Juma’a.
Sanarwar ta bayyana cewa FCTA za ta fara sanya ido sosai kan yadda ake amfani da wuraren taro, otal-otal da sauran gine-ginen jama’a domin tabbatar da cewa ba a amfani da su wajen gudanar da tarukan da za su iya kawo barazana ga zaman lafiya a Abuja ba.
Hukumar ta ce matakin ya zama dole domin kara karfafa tsaro da kuma tallafa wa kokarin jami’an tsaro wajen kare rayuka da dukiyoyin al’umma a Abuja.
A cewar sanarwar, an umurci masu irin wadannan wurare da su tabbatar sun binciki halascin kowace kungiya ko jam’iyya da ke son yin amfani da wurarensu kafin amincewa da bayar da haya.
Ta kara da cewa a wannan lokaci na siyasa, wajibi ne masu wuraren taro da otal-otal su tabbatar suna mu’amala ne kawai da shugabannin jam’iyyun siyasa da hukumar INEC ta amince da su.
Hukumar ta kuma umurci masu wuraren da su rika adana bayanan duk wata mu’amala da suka yi da kungiyoyi ko jam’iyyun siyasa domin saukaka bincike idan bukatar hakan ta taso.
Sanarwar ta gargadi cewa duk wanda ya saba wa wannan umarni zai iya fuskantar kwace takardun mallakar filinsa ko gine-ginensa daga hannun gwamnati.
Wannan mataki dai na zuwa ne a daidai lokacin da ake ci gaba da samun takaddama da rikice-rikicen siyasa a wasu bangarorin Nijeriya gabanin babban zaben shekarar 2027.
