Tsohon Shugaban Jam’iyyar APC na ƙasa, Abdullahi Umar Ganduje, ya bayyana cewa Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso ma ya taɓa kasancewa “yaronsa a siyasa,” yana mai cewa babu buƙatar ‘yan siyasa su riƙa karkatar da tarihi ko rage alaƙar siyasa zuwa batun “uban gida da yaro.”
Ganduje, wanda a halin yanzu yana ƙasa mai tsarki domin gudanar da aikin Hajji, ya bayyana hakan ne yayin da yake mayar da martani kan wasu kalamai Kwankwaso ya yi gare shi, kamar yadda yake ƙunshe a wata sanarwa da Shugaban Ma’aikatansa, Kwamared Muhammad Garba, ya fitar da DClhausa taci karo da’ita.
Tsohon gwamnan jihar Kano ya ce siyasa tana ginuwa ne kan alaƙa, taimako, sadaukarwa da jagoranci, yana mai jaddada cewa kusan kowane babban ɗan siyasa ya amfana da taimako a tafiyarsa ta siyasa.
A cewar sanarwar, Ganduje ya yiwa Kwankwaso tuni cewa yana cikin ‘yan siyasar da suka taimaka masa a farkon tasowarsa a siyasa, musamman a lokacin zaɓen Majalisar Tarayya wanda daga bisani ya kai shi kujerar Mataimakin Kakakin Majalisar Wakilai.
Sanarwar ta ƙara da cewa tun kafin hakan, lokacin da Ganduje ke aiki a matsayin babban ma’aikacin gwamnati a Babban Birnin Tarayya Abuja, daga baya kuma ya zama Kwamishinan Ayyuka, Gidaje da Sufuri a Kano, Kwankwaso kan ziyarce shi a ofisoshinsa da ke Abuja da Kano, har ma wani lokaci yana ɗaukar sa’o’i yana jiransa domin ganawa da shi.
Ganduje ya kuma waiwayi abubuwan da suka faru kafin zaɓen fidda gwani na gwamna a Kano a shekarar 1998, inda ya ce ‘yan siyasa da masu ruwa da tsaki da dama a lokacin sun san cewa shi ne ya lashe zaɓen.
Kazalika manyan ‘yan siyasa da dattawa, waɗanda wasu daga cikinsu har yanzu suna raye, suka roƙe shi da ya hakura domin haɗin kai, tare da amincewa ya tsaya takarar mataimakin gwamna tare da Kwankwaso.
Tsohon gwamnan ya ce duk da waɗannan sauye-sauyen siyasa, shi da Kwankwaso sun yi aiki tare cikin nasara a matsayin gwamna da mataimakin gwamna daga shekarar 1999 zuwa 2003, sannan daga 2011 zuwa 2015, a matsayin abokai da abokan tafiyar siyasa masu kishin ci gaban jihar Kano.
Ya kuma ƙara da cewa, duk da cewa Gwamna Abba Kabir Yusuf ya taɓa zama Mataimaki na Musamman ga Kwankwaso, a yau shi ne halastaccen gwamnan jihar Kano, kuma ya cancanci girmamawa da darajar mukamin da yake kai, har ma daga tsofaffin abokan siyasarsa.
Ya kuma buƙaci ‘yan siyasa a Kano su guji kalaman da za su haddasa rarrabuwar kai, tare da mayar da hankali kan abubuwan da za su ƙarfafa haɗin kai, zaman lafiya da ci gaban jihar.
Tsohon shugaban APC na ƙasa ya kuma roƙi magoya bayan jam’iyyu daban-daban su kwantar da hankalinsu tare da gujewa zafafan martani kan musayar kalaman da aka samu tsakanin shugabannin siyasar jihar.
