DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Tuesday, September 15, 2026
HomeSiyasaZaɓen 2027 zai fi wa Tinubu sauƙi fiye da na 2023 -...

Zaɓen 2027 zai fi wa Tinubu sauƙi fiye da na 2023 – Nyesom Wike

Ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike, ya ce yana ganin zaɓen shugaban ƙasa na 2027 zai kasance mafi sauƙi ga Shugaba Bola Tinubu idan aka kwatanta da zaɓen 2023.

Gidan talabijin na TVC News ya ruwaito Wike ya bayyana hakan ne a ranar Talata yayin da yake duba wuraren da ambaliyar ruwa ke barazana a Maitama, Abuja.

A cewarsa, raunin da ƙungiyoyin adawa suka shiga ya ƙara wa Tinubu ƙarfin gwiwa a siyasance gabanin zaɓen 2027.

“Zaɓen 2027 zai kasance mafi sauƙi ga Shugaban ƙasa idan aka kwatanta da na 2023,” in ji Wike.

Ministan ya ƙara da cewa adawa a yanzu ta samu babban rauni, yana mai cewa, A wannan karon, adawar ta durƙushe, ba ta da matsuguni, ba ta da wani ƙarfi a siyasar Nijeriya.

Wannan furuci na Wike ya zo ne a daidai lokacin da jam’iyyun siyasa ke ci gaba da shirye-shiryen zaɓen 2027, yayin da ake samun sauye-sauyen kawance da sabbin dabarun siyasa a tsakanin ‘yan siyasar kasar.

Da yake magana kan zaɓen gwamnan Osun da aka kammala, Wike ya ce da Shugaba Tinubu ya yi niyyar ganin jam’iyyarsa ta yi nasara a jihar ko ta halin kaka, da ya shiga cikin yakin neman zaɓen, kuma da sakamakon ya bambanta.

“Da Shugaban ƙasa yana son ya ci zaɓen Osun ko ta halin kaka, da na kasance a can, kuma da mun ci zaɓen. Babu abin da gwamnan zai iya yi,” in ji shi.

Duk da cewa Wike ɗan jam’iyyar PDP ne, ya na ci gaba da nuna goyon bayansa ga gwamnatin Shugaba Tinubu, lamarin da ke ci gaba da jawo ce-ce-ku-ce a cikin jam’iyyar da sauran jam’iyyun adawar Nijeriya.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata