DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Tuesday, September 15, 2026
HomeBabban Labari Zan sake buɗe iyakokin Nijeriya idan na zama shugaban kasa - Atiku...

Zan sake buɗe iyakokin Nijeriya idan na zama shugaban kasa – Atiku Abubakar

Ɗan takarar shugabancin Nijeriya a zaɓen 2027 na jam’iyyar ADC, Atiku Abubakar, ya ce zai sake buɗe iyakokin Nijeriya da ƙasashen maƙwabta idan aka zaɓe shi a matsayin shugaban ƙasa.

Atiku ya bayyana hakan ne yayin da yake magana da magoya bayansa a wani faifan bidiyo da aka wallafa a kafafen sada zumunta, wanda ɗaya daga cikin jagororin jam’iyyar ADC, Dele Momodu, ya wallafa ranar Juma’a.

Tsohon mataimakin shugaban ƙasar ya ce rufe iyakokin Nijeriya ya yi mummunan tasiri ga harkokin kasuwanci tsakanin Nijeriya da ƙasashen maƙwabta, tare da ƙara yawan rashin aikin yi musamman tsakanin matasa.

Ya ce jihohin Arewacin Nijeriya suna da iyaka da Kamaru, Chadi, Nijar da Jamhuriyar Benin, kuma mutane da dama na gudanar da halastaccen kasuwancin ƙetare ta waɗannan iyakoki.

Atiku ya ce matasa da dama waɗanda a baya suke gudanar da sana’o’in da jarinsu ya kai miliyoyin naira, tare da ɗaukar wasu mutane aiki, sun rasa sana’o’insu sakamakon rufe iyakokin.

Ya ce rashin aikin yi da matsin tattalin arziki na iya ƙara jefa matasa cikin matsalolin tsaro, yana mai tambayar yadda za a samu tsaro idan an rufe hanyoyin da matasa ke samun abin dogaro da kai.

Atiku ya ce saboda haka, idan aka ba shi dama ya shugabanci ƙasar, zai sake buɗe iyakokin, tare da ɗaukar matakan da suka dace domin hana safarar kayayyaki ba bisa ƙa’ida ba.

Haka kuma, Atiku ya bayyana cewa zai mayar da hankali wajen bunƙasa tashoshin jiragen ruwa da ke Kudancin Nijeriya, domin sauƙaƙa jigilar kayayyaki zuwa sauran sassan ƙasar.

Ya ce a lokacin yaƙin neman zaɓensa na baya, ya tattauna da masu harkar jigilar kayayyaki da kamfanonin bunƙasa tashoshin jiragen ruwa a Turai kan yadda za a inganta tashoshin jiragen ruwa na Kudu da Kudu maso Gabas.

A cewarsa, bunƙasa waɗannan tashoshin zai samar da daidaito wajen shigo da kayayyaki tare da rage tsawon lokaci da kuɗin da ake kashewa wajen jigilar kaya daga Kudancin ƙasar zuwa Arewa.

Atiku ya kawo misalin jigilar kwantena daga Legas zuwa Yola a jihar Adamawa, inda ya ce yana da wata masana’anta, yana mai cewa a halin yanzu jigilar kaya daga Legas zuwa Yola na iya ɗaukar sama da watanni biyu.

Ya ce idan aka bunƙasa tashoshin jiragen ruwa na Calabar, Uyo ko Port Harcourt, za a iya jigilar kwantena zuwa Yola cikin kusan sa’o’i 24, abin da zai rage wa ’yan kasuwa ɗaukar lokaci wajen ɗauko kaya da kuɗi.

Ya kuma ce irin wannan sauyi zai taimaka wajen ƙarfafa kasuwanci, bunƙasa tattalin arziki da samar da ƙarin ayyukan yi ga ’yan Nijeriya.

Iyakokin Nijeriya da wasu ƙasashen maƙwabta an rufe su sosai a shekarar 2019 a lokacin gwamnatin tsohon Shugaba Muhammadu Buhari, wadda ta ce matakin ya kasance wani yunkuri na yaƙi da fasa-kwauri da kuma ƙarfafa noman cikin gida.

Gwamnatin Buhari ta fara sake buɗe wasu manyan iyakoki a shekarar 2020, yayin da gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ita ma ta sake buɗe wasu hanyoyin kan iyaka a shekarar 2026, ciki har da iyakar Tsamiya da Jamhuriyar Benin da kuma hanyar Kamba da ke haɗa Nijeriya da Nijar.

Sai dai har yanzu wasu iyakokin ƙasar na ci gaba da kasancewa ƙarƙashin takunkumi ko tsauraran matakan kula da zirga-zirga.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata