Sanata Ali Ndume, mai wakiltar mazabar Borno ta Kudu, ya ce wasu daga cikin jami’an da ke aiki a fadar shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ba su cancanci mukaman da suke riƙe da su ba, yana mai cewa rashin ƙwarewarsu na janyo wa shugaban ƙasar da gwamnatinsa abin kunya.
Ndume ya yi gargadin cewa matuƙar Shugaba Tinubu bai ɗauki kwakkwaran mataki kan irin waɗannan jami’ai ba, za su ci gaba da jefa shi cikin matsaloli tare da ɓata masa suna.
Sanatan ya bayyana hakan ne ranar Laraba yayin wata hira da aka yi da shi a gidan talabijin na Arise, inda ya ce ya fara damuwa ne bayan gano wata hukumar gwamnati ta bogi da ke aiki a ƙarƙashin kulawar gwamnatin tarayya.
Ya ce da a ce akwai ƙwararrun jami’ai a wuraren da suka dace a cikin gwamnatin, da ba a samu irin wannan matsala ba.
Ya kuma yaba wa shugaban ƙasa kan dakatar da wani babban sakataren gwamnati bayan binciken da ICPC ta gudanar.
Ndume ya ce: “Abin da ke damuna shi ne yadda akwai mutane marasa cancanta da yawa da suka mamaye fadar shugaban ƙasa, matukar bai ɗauki mataki ba, za su ci gaba da jefa shi cikin matsala.”
Sanatan ya kuma soki yadda wasu masu magana da yawun shugaban ƙasa ke mayar da martani ga masu sukar gwamnati, yana mai cewa maimakon zagi ko kiran mutane, ya kamata a mayar da hankali kan abubuwan da suka gabatar na suka kan manufofin gwamnati.
A kan cire tallafin man fetur, Ndume ya ce yana goyon bayan matakin da gwamnatin Tinubu ta ɗauka na cire tallafin, duk da cewa ya amince cewa matakin ya haifar da tsananin wahala ga ’yan Nijeriya.
Ya ce cire tallafin na daga cikin manyan matakai masu wahala da Shugaba Tinubu ya ɗauka, amma matsalar ita ce tasirin manufofin ya jefa jama’a cikin matsin tattalin arziki.
Ndume ya ce gwamnati na buƙatar ta fi mayar da hankali wajen bayyana wa ’yan Nijeriya abin da take yi da kuma yadda manufofinta za su amfanar da su, maimakon jami’an gwamnati su riƙa kai hari ga ’yan adawa.
A cewarsa, ’yan adawa ma ya kamata su gabatar da manufofi da shirye-shirye tare da gamsar da ’yan Nijeriya cewa hanyoyin da suke bayarwa za su iya aiki.
