Dan takarar shugabancin Nijeriya a jam’iyyar NDC, Peter Obi, ya bayyana cewa idan aka zaɓe shi a zaɓen shekarar 2027, gwamnatinsa za ta yi sulhu da tattaunawa da duk wani ɗan bindiga ko mai aikata laifi da ya nuna aniyar ajiye makami da rungumar zaman lafiya.
Obi ya bayyana hakan ne yayin wata hira da aka yi da shi, inda ya gabatar da wasu shirye-shirye da yake da su domin yin sulhu wajen magance matsalolin tsaro da haɗa kan al’ummar Nijeriya.
A cewarsa, duk wanda yake son zaman lafiya ta haryar sulhu, gwamnatinsa za ta tattauna da shi domin samar da mafita mai ɗorewa, sai dai ya jaddada cewa waɗanda suka zaɓi ci gaba da ta’addanci da tashin hankali za su fuskanci fushin gwamnati.
Tsohon gwamnan jihar Anambra ya ce akwai buƙatar samar da hanyoyin gyara rayuwar waɗanda suka tuba cikin al’umma domin su zama masu amfani ga ƙasa maimakon ci gaba da aikata laifi.
Ya bayyana cewa ci gaban kowace al’umma na samuwa ne idan an ba mutane damar gyara kura-kuransu tare da komawa rayuwa cikin tsari.
Ya kuma ba da misalin wata jami’a a ƙasar Amurka da ya ziyarta, inda ya ce wasu daga cikin manyan jami’an makarantar sun taɓa zama a gidan yari kafin daga baya suka gyara rayuwarsu.
Obi ya danganta matsalar tsaro da rashin haɗin kai a ƙasa, yana mai cewa dole ne kowace ƙabila, yanki da addini su ji suna da matsayi da wakilci a cikin harkokin gwamnati.
Ya ce manufarsa ita ce gina Nijeriya mai adalci da daidaito, inda babu wani yanki ko ƙabila da za su ji an ware su daga anfani da damar ƙasa.
Sai dai kalamansa sun sake tayar da muhawara kan ko sulhu da tattaunawa da masu ɗauke da makamai hanya ce mafi dacewa wajen magance matsalolin tsaro ko kuwa ya kamata a fi mayar da hankali kan matakan soji da doka.
Masu goyon bayan wannan tsari na ganin cewa tattaunawa na iya taimakawa wajen rage tashin hankali da dawo da zaman lafiya, yayin da masu adawa ke cewa hakan na iya ƙarfafa masu aikata laifuka da kuma rage tasirin yaƙin da jami’an tsaro ke yi da su.
A kwanakin baya, wasu ‘yan majalisa da lauyoyi sun nuna damuwa cewa yin sulhu da ƙungiyoyin masu aikata ta’addanci na iya saɓawa wasu dokoki tare da aika saƙon da ba daidai ba ga masu laifi.
