DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Friday, May 15, 2026
HomeLabaraiƊan Sule Lamido ya karɓi fom ɗin takarar gwamnan Jigawa a PDP

Ɗan Sule Lamido ya karɓi fom ɗin takarar gwamnan Jigawa a PDP

Ɗan Sule Lamido ya karɓi fom ɗin takarar gwamnan Jigawa a PDP

Mustapha Sule Lamido, ɗan tsohon gwamnan Jihar Jigawa Sule Lamido, ya shiga takarar gwamna bayan karɓar fom ɗin takarar jam’iyyar PDP domin zaɓen 2027.

Kamar yadda rahoton ya nuna, Mustapha Lamido ya miƙa fom ɗin ga kwamitin gudanarwar PDP na jihar da sauran masu ruwa da tsaki ranar Talata a Dutse domin neman amincewarsu.

DCL Hausa ta ruwaito cewa tsohon ɗan takarar gwamnan PDP a zaɓen 2023 ya ce ya kammala dukkan tuntuba, kuma yanzu yana neman goyon bayan jam’iyyar domin ya zama ɗan takararta.

Ya ce, “Mu cikakkun mambobin PDP ne kuma muna da yakinin jam’iyyarmu na da ƙarfin magance matsalolinta da kuma matsalolin Jigawa.”

Mustapha ya bayyana cewa PDP ce kaɗai jam’iyyar da ke da tarihin aiwatar da ayyuka da shirye-shiryen da ke amfani ga jama’a.

Ya kuma zargi jam’iyyun da suka karɓi mulki bayan PDP da gaza cika alkawura, yana mai cewa matsalolin tattalin arziki, tsaro da zamantakewa sun ƙaru.

Ɗan takarar ya buƙaci mambobin PDP a Jigawa su mara masa baya gabanin zaɓen 2027, yana mai alƙawarin ci gaba da kare manufofin jam’iyyar na kishin ƙasa da hidimtawa jama’a.

Ukashatu Ibrahim Wakili
Ukashatu Ibrahim Wakilihttps://dclhausa.com
Ukashatu Wakili, Mataimakin Manajan Edita kuma Mai Kula da Shirin Koyon Sanin Makamar Aiki ne a DCL Hausa. A matsayinsa na ƙwararren ɗan jarida yana tsara ayyukan rediyo da kafafen sada zumunta, fassarar labarai, da tabbatar da sahihancin bayanai. Yana jagorantar shirin horaswa ga masu koyon aiki tare da kula da ingancin rubuce-rubuce da shirye-shiryen gidan jaridar.
RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata