DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Wednesday, July 8, 2026
HomeLabaraiSahihin zaɓen 2027 zai ƙara wa dimokuraɗiyyar Nijeriya ƙarfi - Jakadan Birtaniya

Sahihin zaɓen 2027 zai ƙara wa dimokuraɗiyyar Nijeriya ƙarfi – Jakadan Birtaniya

Babban Jakadan Birtaniya a Nijeriya, Richard Montgomery, ya ce sahihanci da amincin zaɓen shekarar 2027 zai kasance muhimmin ginshiƙi wajen tabbatar da ci gaba da amincewar jama’a da tsarin dimokuraɗiyyar Nijeriya.

Montgomery ya bayyana hakan ne ranar Juma’a a Abuja yayin taron tattaunawa da baje kolin hotuna na Ranar Dimokuraɗiyya ta 12 ga Yuni, wanda ƙungiyar Nigeria Civil Society Situation Room ta shirya.

Kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito, jakadan ya ce gudanar da zaɓe cikin lumana, gaskiya da kuma bai wa kowa damar shiga zaɓe zai buƙaci haɗin gwiwar duk masu ruwa da tsaki, musamman ƙungiyoyin fararen hula. Ya ce sahihin zaɓe ba kawai zai ƙarfafa dimokuraɗiyya ba ne, har ma zai taimaka wa Nijeriya ci gaba da jagoranci a nahiyar Afirka.

Montgomery ya kuma yi kira da a ƙara bai wa mata, matasa, masu buƙata ta musamman da sauran rukunonin da ake ganin ba sa samun cikakkiyar dama muhimmiyar rawa a harkokin zaɓe. Ya ce yadda waɗannan rukunoni za su shiga cikin tsarin siyasa zai taimaka wajen ƙarfafa amincewar jama’a da sakamakon zaɓe.

Ya kuma jaddada cewa gwamnatin Birtaniya za ta ci gaba da tallafa wa ƙoƙarin da ake yi na inganta cibiyoyin dimokuraɗiyya da tabbatar da gaskiya a zaɓe.

A nasa ɓangaren, Wanda ya Shirya Taron Situation Room, Clement Nwankwo, ya nuna damuwa kan wasu alamomi da ya ce na iya kawo cikas ga tsarin zaɓen 2027, yayin da tsohon ɗan Majalisar Wakilai, Abdul Oroh, ya bukaci matasa su shiga siyasa tun da wuri domin ƙarfafa dimokuraɗiyya a ƙasar.

Ukashatu Wakili
Ukashatu Wakilihttps://dclhausa.com
Ukashatu Wakili, Mataimakin Manajan Edita kuma Mai Kula da Shirin Koyon Sanin Makamar Aiki ne a DCL Hausa. A matsayinsa na ƙwararren ɗan jarida yana tsara ayyukan rediyo da kafafen sada zumunta, fassarar labarai, da tabbatar da sahihancin bayanai. Yana jagorantar shirin horaswa ga masu koyon aiki tare da kula da ingancin rubuce-rubuce da shirye-shiryen gidan jaridar.
RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata