Shugaban kungiyar dattawan Arewa kuma tsohon mataimakin shugaban jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya, Farfesa Ango Abdullahi, ya ce Arewacin Nijeriya na fuskantar matsaloli ne saboda rasa ƙima da manufofin shugabanci da suka kasance ginshiƙin ci gabanta a baya.
Jaridar Punch ta ruwaito cewa Farfesa Ango Abdullahi ya bayyana hakan ne a ranar Asabar, yayin taron tunawa da marigayi Janar Hassan Usman Katsina karo na uku da aka gudanar a Arewa House da ke Kaduna.
Farfesa Ango Abdullahi ya ce Arewa, wadda a baya aka san ta da ladabi, gaskiya da jajircewa, ta rasa waɗannan ƙimomi. Ya ce idan da ba a yi watsi da dabi’un da aka gada daga iyaye da shugabannin farko ba, da yankin bai tsinci kansa a halin da yake ciki a yau ba.
Ya ƙara da cewa duk da yadda wasu biranen Arewa suka bunƙasa ta fuskar gine-gine, halaye irin su riƙon amana, sadaukarwa, kishin ƙasa da shugabanci na gari sun ragu. Ya ce marigayi Janar Hassan Usman Katsina na cikin shugabannin da suka yi fice wajen nuna gaskiya, riƙon amana da sadaukar da kai wajen yi wa al’umma hidima, yana mai cewa idan aka koma kan irin waɗannan ƙimomi, Arewa za ta iya samun sauyi.
A nasa jawabin, Dokta Usman Bugaje ya ce Arewa ta shafe shekaru tana fuskantar koma bayan tattalin arziki, matsalar tsaro da rauni saboda kaucewa irin salon shugabanci da Janar Hassan Usman Katsina da takwarorinsa suka wakilta.
Ya ce samar da abinci na ci gaba da raguwa, dubban mutane sun rasa muhallansu, tattalin arziki na durƙushewa, talauci ya ƙaru, yayin da ilimi da kiwon lafiya suka fuskanci matsaloli.
An shirya taron tunawa da marigayi Janar Hassan Usman Katsina ne domin tuna irin gudummawar da ya bayar tare da tattauna batutuwan shugabanci, mulki da makomar Arewacin Nijeriya.
