DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Monday, September 21, 2026
HomeSiyasaAtiku ya kalubalanci Obasanjo ya fito fili ya nuna goyon bayansa ga...

Atiku ya kalubalanci Obasanjo ya fito fili ya nuna goyon bayansa ga Tinubu

Tsohon Mataimakin Shugaban Nijeriya kuma ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar ADC a zaɓen 2027, Atiku Abubakar, ya kalubalanci tsohon Shugaban Ƙasa, Cif Olusegun Obasanjo, da ya fito fili ya bayyana wanda yake marawa baya a zaɓen 2027, maimakon amfani da tsoffin zarge-zarge wajen sauya ra’ayin jama’a.

Premium Times ta ruwaito cewa Atiku ya bayyana hakan ne cikin wata sanarwa da mai taimaka masa kan harkokin yaɗa labarai, Phrank Shaibu, ya fitar a ranar Juma’a. Hakan ya biyo bayan ikirarin da Obasanjo ya yi cewa Atiku ya bai wa marigayi Kakakin Majalisar Wakilai, Ghali Na’Abba, Naira miliyan biyar domin ya jagoranci yunƙurin tsige shi daga mulki a lokacin da suke aiki tare.

Atiku ya ce sake fito da wannan zargi a wannan lokaci na da alaƙa da yadda siyasar zaɓen 2027 ke ƙara ɗaukar zafi.

A cewarsa, “Abin da ake son yi shi ne a bata min suna tare da bai wa ɗan uwan tsohon shugaban ƙasa wata dama ta siyasa da bai cancanta ba. Amma ‘yan Nijeriya sun fi haka fahimta.”

Atiku ya kuma ce idan har Obasanjo ya riga ya zaɓi ɗan takarar da yake goyon baya, ya kamata ya bayyana hakan a fili.

“Ya kamata kawai ya bayyana wanda yake goyon baya, ya bar ‘yan Nijeriya su yi hukunci bisa cancanta, maimakon ƙoƙarin rinjayar ra’ayin jama’a ta hanyar zarge-zargen da ba za a iya tabbatar da su ba.”

Ya kuma tambayi dalilin da ya sa Obasanjo bai yi irin wannan zargi ba tun lokacin da marigayi Ghali Na’Abba yake raye.

Idan za a iya tunawa dai alaƙar siyasa tsakanin Obasanjo da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ta yi tsami tsawon shekaru, tun daga rikicin ƙirƙirar ƙananan hukumomi a Legas a 2003 zuwa adawar Tinubu ga yunƙurin wa’adi na uku da ake dangantawa da Obasanjo. Haka kuma, Obasanjo ya goyi bayan Peter Obi a zaɓen 2023, sannan ya ci gaba da sukar manufofin tattalin arzikin gwamnatin Tinubu.

Ukashatu Wakili
Ukashatu Wakilihttps://dclhausa.com
Ukashatu Wakili is a journalist and media professional serving as Deputy Managing Editor and Internship Coordinator at DCL Hausa. He has extensive experience in broadcast and digital journalism, with expertise in news reporting, editorial production, newsroom coordination and journalist training. He holds a B.Sc. in Mass Communication from Usmanu Danfodiyo University, Sokoto.
RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata