Shugaban Nijeriya Bola Ahmed Tinubu, ya ce tuni ’yan Najeriya suka fara ganin raguwar kudin sufuri sakamakon amfani da makamashi mai rahusa, musamman iskar gas ta CNG.
Shugaban ya bayyana hakan ne yayin da yake bayar da bayani kan alkawarin da ya yi na ganin an rage kudin sufuri ga ’yan Najeriya daga ranar 1 ga Oktoba 2026.
A ranar 27 ga Agusta, Tinubu ya gana da gwamnonin jihohi 36, inda suka tattauna matakan da za a dauka domin rage kudin sufuri a fadin kasar tare da rage wa ’yan Najeriya radadin tsadar rayuwa.
Bayan taron ne aka kafa kwamitin aiwatar da shirin sufuri mai saukin kudi na CNG na kasa karkashin kungiyar Gwamnonin Nijeriya.
Tinubu ya ce kwamitin, da PI-CNG & EV, jihohi da sauran masu ruwa da tsaki, sun riga sun fara aiki wajen gano muhimman hanyoyin sufuri, tantance matakan da suka dace da kuma samar da abubuwan da ake bukata domin rage kudin sufuri.
Ya ce a Borno, motocin sufuri masu amfani da CNG da wutar lantarki na jigilar fasinjoji a wasu hanyoyi kan kudi N50 zuwa N100, yayin da masu motocin kasuwanci ke karbar tsakanin N300 zuwa N600.
A Kaduna kuma, motoci 100 masu amfani da CNG na jigilar mutane kyauta a manyan hanyoyin jihar.
A shekararsu ta farko, motocin sun dauki fasinjoji kusan miliyan 3.2, lamarin da ya ceci ’yan kasar sama da Naira biliyan 3.5 na kudin sufuri.
A Oyo kuwa, motocin CNG da aka tura karkashin kamfanin Pacesetter Transport sun rage kudin mota daga Legas zuwa Ibadan daga kusan N8,000 zuwa N3,200 a lokacin fara shirin.
A Adamawa, amfani da motocin da ke aiki da madadin makamashi ya rage kudin sufuri da kusan kashi 50 cikin 100, daga N8,000 zuwa N4,000.
A Enugu kuma, tura motocin CNG 100 ya sa kudin mota daga Enugu zuwa Nsukka ya ragu daga N2,500 zuwa N1,500.
A Plateau, motocin da gwamnatin jihar ke tallafawa na jigilar fasinjoji kusan 13,000 a kowace rana kan N200, yayin da masu sufuri masu zaman kansu ke karbar sama da N500.
Shugaban ya kara da cewa, ta hanyar hadin gwiwa da Kungiyar Ma’aikatan Sufuri ta Nijeriya, NURTW, fasinjojin da ke amfani da motocin kasuwanci da aka mayar da su masu amfani da CNG a wasu hanyoyin Abuja suna samun rangwamen kudin mota da kashi 40 cikin 100.
Ya ce kudin mota daga Area 1 zuwa Gwagwalada ya ragu daga N1,500 zuwa N900, yayin da daga Nyanya ya koma daga N700 zuwa N420, sannan daga Wuse ya ragu daga N400 zuwa N240.
Tinubu ya ce a jihar Neja, fasinjojin da ke tafiya daga Suleja zuwa Abuja na biyan N550 maimakon kusan N800.
A Abia kuma, an tura motocin bas masu amfani da wutar lantarki 40, inda gwamnati ke tallafa musu da kashi 50 cikin 100 na kudin sufuri.
Ya ce wannan ba wani shiri ne da ake hasashen zai faru nan gaba ba, domin tuni ’yan Najeriya ke amfana da raguwar kudin sufuri.
Tinubu ya yaba wa gwamnonin da suka fara amfani da CNG wajen sufuri, amma ya ce akwai sauran ayyuka da ya kamata a gudanar.
Ya kuma yi alkawarin cewa gwamnatin tarayya za ta taimaka wa jihohin wajen fadada shirye-shiryen.
Shugaban ya ce matsalar makamashi a duniya ta sake janyo karin farashin man fetur da dizal, wanda hakan ke kara kudin sufuri a kasashe daban-daban.
Ya ce Nijeriya ba za ta iya sarrafa abubuwan da ke faruwa a kasuwar makamashi ta duniya ba, amma kasancewar kasar na da dimbin iskar gas ya ba ta damar rage dogaro da man fetur.
Tinubu ya ce a cikin shekaru uku da suka gabata, gwamnatinsa ta zuba jari wajen gina tsarin sufuri mai amfani da CNG a fadin Nijeriya, inda zuwa yanzu aka mayar da motoci sama da 120,000 zuwa masu amfani da CNG.
Ya ce akwai cibiyoyin sauya motocin zuwa CNG sama da 400 da aka amince da su, da kuma tashoshin cike CNG sama da 90 a fadin kasar, kuma adadin na ci gaba da karuwa.
Shugaban ya ce bai kamata a koma tsarin tallafin man fetur da ya ce ya janyo asarar tiriliyoyin naira ga kasa ba, maimakon a hanzarta amfani da hanyoyin samar da makamashi masu rahusa da ake ginawa a cikin gida.
Ya ce a Edo, motocin bas 50 masu amfani da CNG na aiki, yayin da Kano ta mayar da sama da motocin kasuwanci 1,000 zuwa masu amfani da CNG tare da fadada cibiyoyin sauya motoci da tashoshin cike CNG.
Tinubu ya ce jihohin Delta, Kwara da Legas na fadada ayyukan sufuri masu amfani da CNG, yayin da Akwa Ibom ta karbi motocin bas 50 masu amfani da CNG domin fara harkokin kasuwanci.
Shugaban ya bukaci dukkan jihohin kasar su ci gaba da kokarin rage kudin sufuri kafin ranar 1 ga Oktoba, tare da yin aiki tare da kungiyoyin ma’aikatan sufuri da masu motocin kasuwanci.
Ya ce ya kamata jihohi su tallafa wajen sauya motocin zuwa CNG, samar da kayayyakin more rayuwa da kuma tabbatar da cewa rage kudin makamashi ya kai ga ’yan kasa ta hanyar rage kudin da suke biyan sufuri.
Tinubu ya ce Nijeriya na da iskar gas, kuma ana gina abubuwan more rayuwa da ake bukata domin amfani da shi, don haka lokaci ya yi da za a kara sauri wajen fadada shirin domin karin ’yan Najeriya su amfana da raguwar kudin sufuri a kullum.
