DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Monday, September 21, 2026
HomeLabaraiTinubu ya buƙaci likitocin Nijeriya mazauna ƙasashen waje su dawo gida

Tinubu ya buƙaci likitocin Nijeriya mazauna ƙasashen waje su dawo gida

Shugaban Nijeriya Bola Ahmed Tinubu, ya buƙaci likitocin Nijeriya da sauran ƙwararrun ma’aikatan lafiya da ke zaune a ƙasashen waje su dawo gida domin ba da gudummawarsu wajen inganta harkar kiwon lafiya a ƙasar.

Shugaba Tinubu ya bayyana hakan ne lokacin da ya karɓi baƙuncin tawagar Ƙungiyar Likitocin Nijeriya mazauna ƙasashen waje tare da shugabar hukumar ‘yan Nijeriya mazauna kasashen waje (NiDCOM), Abike Dabiri-Erewa, a fadar shugaban da ke Abuja, a wani ɓangare na bikin Ranar ‘Yan Nijeriya Mazauna Ƙasashen Waje ta 2026.

Shugaban ƙasar ya ce Nijeriya na buƙatar ilimi, ƙwarewa, sabbin dabaru da kishin ƙasa na ƙwararrun ‘yan ƙasar da ke ƙasashen waje domin gina tsarin kiwon lafiya mai ƙarfi. Ya kuma yabawa tawagar bisa ayyukan jinya kyauta da suka gudanar a yankuna daban-daban na Nijeriya.

Tinubu ya ce gwamnatin tarayya na zuba jari a ilimin likitanci, bincike, fasahar kiwon lafiya da inganta walwalar ma’aikatan lafiya domin rage matsalar ƙaura zuwa ƙasashen waje.

A nata jawabin, Shugabar NiDCOM, Abike Dabiri-Erewa, ta ce tawagar ta zo ne domin tallafa wa shirin gwamnatin Tinubu na inganta harkar lafiya a Nijeriya.

Ta ce yawancin membobinsu sun sami horo ne a Nijeriya kuma suna son mayar wa ƙasar da gudummawar da ta taimaka musu suka kai matsayin da suke a yau.

Ministar Lafiya ta Ƙasa, Dokta Iziaq Salako, ta ce matakin da ƙwararrun likitocin suka ɗauka ya nuna yadda shirin Renewed Hope Agenda ya samu karɓuwa har a wajen Nijeriya. Ya ce yawancin ƙwararrun da ke ƙasashen waje sun nuna shirinsu na dawo da iliminsu da gogewarsu domin taimaka wa tsarin kiwon lafiyar ƙasar.

Ukashatu Wakili
Ukashatu Wakilihttps://dclhausa.com
Ukashatu Wakili is a journalist and media professional serving as Deputy Managing Editor and Internship Coordinator at DCL Hausa. He has extensive experience in broadcast and digital journalism, with expertise in news reporting, editorial production, newsroom coordination and journalist training. He holds a B.Sc. in Mass Communication from Usmanu Danfodiyo University, Sokoto.
RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata