Ƙungiyar SERAP mai fafutikar tabbatar da gaskiya da adalci ta buƙaci Shugaba Bola Ahmed Tinubu da ya umarci hukumomin da abin ya shafa su bayyana yadda aka kashe sama da naira biliyan 78.8 na kuɗin gwamnati da aka karkatar ko kuma aka kashe ba bisa ƙa’ida ba a ƙarƙashin shirin raba tallafin kuɗi na rage raɗaɗi.
Jaridar Punch ta bayyana cewa mataimakin daraktan ƙungiyar ta SERAP, Kolawole Oluwadare, ne ya bayyana hakan a cikin wata wasiƙa mai kwanan watan 5 ga watan Satumban 2026 da aka fitar a ranar Lahadi, inda ya buƙaci shugaban ƙasar da ya umarci Ma’aikatar Jinƙai da Ofishin Raba Tallafin Kuɗi na Ƙasa (NCTO) da su fitar da cikakkun bayanan yadda aka kashe naira biliyan 33.751 a shekarar 2023.
SERAP ta bayyana cewa waɗannan zarge-zarge sun fito ne daga rahoton shekara-shekara na 2024 na babban mai binciken kuɗi na ƙasa da aka wallafa a ranar 7 ga watan Agustan 2026, wanda ya rufe hada-hadar kuɗi tsakanin watan Janairun 2023 zuwa watan Disambar 2024.
A cewar rahoton binciken, ofishin NCTO ya raba naira biliyan 33.751 ga gidaje da mutum 3,295,207 a jihohi 35 a shekarar 2023 ba tare da wata cikakkiyar shedar da ke nuna mutanen sun karɓi kuɗin ba, sannan an gaza gabatar da bayanan katin biyan kuɗi na REMITA domin tantance waɗanda suka amfana na gaskiya.
Rahoton ya kuma bayyana cewa NCTO ta biya naira biliyan 4.616 kan wasu ɓangarori ba tare da hujjojin kashe kuɗi ba, inda babban mai binciken ya nuna fargabar cewa an karkatar da kuɗaɗen, tare da biyan naira biliyan 36.74 a watan Disambar 2023 ba tare da binciken cikin gida ba. Haka kuma an samu zargin rashin bin ƙa’ida na naira biliyan 2.55 a ofishin daidaita tsare-tsaren tallafin jama’a (NASSCO).
Ƙungiyar ta SERAP ta gargaɗi gwamnatin tarayya cewa idan ba ta ɗauki mataki kan binciken tare da gurfanar da waɗanda ke da hannu a ciki ba a tsawon kwanaki bakwai, ƙungiyar za ta shigar da ƙara a kotun ƙungiyar ECOWAS da kuma kwamitin bincike na Bankin Duniya domin tilasta wa gwamnati bin doka da kare haƙƙin al’umma.
