Ministan harkokin cikin gida, Dokta Olubunmi Tunji-Ojo, ya ce iyakokin ƙasar Nijeriya ba a rufe suke ba, don haka ba za a iya cewa za a “sake buɗe” su ba kamar yadda tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, ya yi alkawarin yi idan ya lashe zaɓen shugaban ƙasa na 2027.
Ministan ya bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Asabar, yayin da yake mayar da martani kan shirin Atiku na sake buɗe iyakokin ƙasa, kamar yadda jaridar Punch.
Tunji-Ojo ya ce hukumar kula da shige da fice ta Nijeriya ce ke kula da harkokin iyaka da shige da fice, kuma gwamnatin yanzu na ci gaba da ba da damar zirga-zirga da kasuwanci ta kan iyakokin ƙasar cikin tsari.
Tunji-Ojo ya ce gwamnatin da ta gabata ta sake buɗe manyan iyakoki huɗu, Seme, Illela, Maigatari da Mfum, a ranar 16 ga Disamba 2020, yayin da aka sake buɗe Idiroko da Ikom domin kayayyaki da ayyuka a ranar 20 ga Afrilu 2022.
Ya ƙara da cewa gwamnatin Shugaba Bola Tinubu ta sake buɗe Kamba da Tsamiya a Jihar Kebbi a watan Fabrairu 2026, waɗanda ke haɗa Nijeriya da Jamhuriyar Nijar da Benin.
Ministan ya kuma ƙalubalanci ikirarin cewa an rufe iyakokin da Nijeriya ke da su da Kamaru, Chadi, Nijar da Benin saboda manufar kasuwanci ta shekarar 2019. Ya ce rufe Banki da Amchidé da ke kan iyakar Kamaru ya samo asali ne daga matsalar tsaro da Boko Haram ta haddasa tun 2014.
Ya ce an sake buɗe waɗannan mashigar a shekarar 2019, yayin da aka sake buɗe Fotokol da Gambaru a 2021 bayan haɗin gwiwar sojojin Nijeriya, Kamaru, Nijar da Chadi.
Sai dai Tunji-Ojo ya amince cewa wasu mashigar kan iyaka musamman a arewacin ƙasar ba sa aiki yadda ya kamata, saboda matsalolin tsaro da ke ci gaba da faruwa a wasu yankunan.
Ya ce sake buɗe mashigar iyaka ba tare da inganta tsaro ba na iya jefa ’yan kasuwa da mazauna yankunan kan iyaka cikin ƙarin haɗari. Ya ƙara da cewa ingantaccen kula da iyaka ya kamata ya haɗa tsaro, takardun shaida, bin dokokin kwastam da sauƙaƙa kasuwanci.
Tunji-Ojo ya bukaci Atiku ya bayyana dalla-dalla sabon tsarin da yake son amfani da shi kan iyakokin Nijeriya idan ya zama shugaban ƙasa, maimakon haɗa matsalolin kasuwanci, tsaro da ababen more rayuwa wuri guda.
Atiku, wanda ya nemi shugabancin Nijeriya sau shida tun shekarar 1993, ya kuma yi alkawarin bunƙasa tashoshin jiragen ruwa a yankin Kudu maso Kudu da Kudu maso Gabas domin magance abin da ya kira rashin daidaito wajen shigo da kaya da sufuri.
