Shugaban Kamfanin MTN Nijeriya, Karl Toriola, ya kare farashin data da kamfanonin sadarwa ke caji a ƙasar, yana mai cewa Nijeriya na cikin ƙasashe huɗu da ke da mafi ƙarancin farashin data a duniya.
Toriola ya bayyana hakan ne yayin da ake ci gaba da karɓar korafe-korafe daga wasu masu amfani da layukan sadarwa kan tsadar data da saurin ƙarewarta.
Shugaban MTN ya ce sabanin yadda wasu ke gani, farashin data a Nijeriya na daga cikin mafi araha idan aka kwatanta da sauran ƙasashe na duniya.
