DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Thursday, October 8, 2026
HomeBabban Labari Gwamnatin Tinubu za ta saukar da farashin man fetur na wata guda

Gwamnatin Tinubu za ta saukar da farashin man fetur na wata guda

Gwamnatin Nijeriya ta bayyana wani shiri da zai bai wa ’yan ƙasar damar cin moriyar rangwamen farashin man fetur na tsawon wata guda, a wani mataki da aka ce yana da nufin rage wa al’umma raɗaɗin tsadar sufuri.

Gwamnatin ta bayyana shirin ne yayin da farashin man fetur ke ci gaba da yin tasiri kan tsadar sufuri da sauran kayayyaki da ayyuka a faɗin ƙasar kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Ministan Kudi da Ministan tattalin arziki Taiwo Oyedele ya bayyana haka a lokacin da yake jawabi a taron Manema labarai a Abuja ranar Alhamis.

Yace ” za a samu rangwame a fetur nan da kwanaki 30 Musamman ga masu zirga-zirga, kamar yadda Jaridar Daily trust ta ruwaito.

Ya ƙara da cewa Gwamnatin Nijeriya za ta tattauna kan kuɗaɗen jigilar man fetur wanda za a riƙa yin dubi akan sa a kowane wata.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata