DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Tuesday, July 7, 2026
HomeLabaraiMajalisar tattalin arzikin Nijeriya ta amince da kashe N83bn don dakile ambaliyar...

Majalisar tattalin arzikin Nijeriya ta amince da kashe N83bn don dakile ambaliyar ruwa

Majalisar tattalin arziki ta Nijeriya (NEC) ta amince da ware Naira biliyan 83.21 domin aiwatar da shirin ‘Anticipatory Action Task Force’, da nufin rage illar ambaliyar ruwa da sauran bala’o’in da ke da alaka da sauyin yanayi a fadin Nijeriya.

An cimma matsayar ne a taron majalisar karo na 158 da mataimakin shugaban kasa Kashim Shettima, ya jagoranta a Fadar Villa da ke Abuja.

Gwamnan Jihar Cross River, Bassey Otu, ya shaida wa manema labarai cewa majalisar ta amince da wannan kudi ne bayan ta karbi bukatar Naira biliyan 166.42 da ministan kasafi da tsare-tsaren tattalin arziki, Atiku Bagudu, ya gabatar, kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.

Ya ce majalisar ta yanke shawarar amincewa da rabin adadin kudin da aka nema, tare da alkawarin sake duba tsarin a tarurruka masu zuwa.

Da yake bayani kan dalilin rage kudin da kashi 50 cikin 100, Otu ya ce hakan wani mataki ne na fara aiwatar da shirin bisa la’akari da karancin albarkatu, ba wai saboda rashin fahimtar gaggawar bukatar ba.

Shi ma Gwamnan Jihar Plateau, Caleb Mutfwang, ya ce wannan tallafi shi ne matakin farko na shirin, wanda zai mayar da hankali kan daukar matakan gaggawa da kuma samar da hanyoyin warware matsalar na dogon lokaci.

Ya kara da cewa daga cikin hanyoyin akwai gina madatsun ruwa domin rage matsalar ambaliya da ke faruwa sakamakon sakin ruwa daga ‘Lagdo Dam’ a kasar Kamaru.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata