DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Wednesday, September 23, 2026
HomeLabaraiDamina na ƙara ta’azzara cututtuka da yunwa a Zamfara — MSF

Damina na ƙara ta’azzara cututtuka da yunwa a Zamfara — MSF

Ƙungiyar agajin lafiya ta duniya Médecins Sans Frontières wadda aka fi sani da MSF, ta bayyana damuwa kan yadda damina ke ƙara jefa al’ummar jihar Zamfara cikin matsanancin hali na cututtuka da ƙarancin abinci.

A wata sanarwa da ƙungiyar ta fitar ranar Litinin, ta ce daminar bana na ƙara haddasa yawaitar cututtuka irin su zazzabin cizon sauro, kwalara, taifod da kuma matsanancin tamowa musamman a yankunan da rikice-rikicen tsaro suka daɗe suna addaba.

Jaridar Punch ta ambato MSF ta bayyana cewa ambaliyar ruwa, rashin tsafta da cunkoson jama’a a sansanonin ‘yan gudun hijira na ƙara saurin yaɗuwar cututtuka, yayin da matsalar yunwa da ƙarancin samun kulawar lafiya ke jefa dubban mutane cikin haɗarin mutuwa.

Manajan ayyukan jinya na asibitin MSF da ke Zamfara, Sani Adamu, ya ce damina ta zama tamakar kakar mace-mace ga iyalai da dama da tuni suka rasa matsugunansu da hanyoyin samun abinci sakamakon hare-haren ‘yan bindiga.

Ya ce kafewar ruwa bayan ambaliya na zama mafakar sauro, abin da ke ƙara yawan masu fama da zazzabin cizon sauro, yayin da gurɓataccen ruwa ke haddasa barkewar kwalara da sauran cututtukan da ake ɗauka ta ruwa.

MSF ta ce a shekarar 2025 kaɗai ta yi wa mutum 136,778 maganin zazzabin cizon sauro a Zamfara, tare da kula da mutum 13,877 masu fama da kwalara.

Ƙungiyar ta kuma bayyana ƙarin damuwa kan yawaitar matsalolin cutar taifod musamman a tsakanin yara, inda ta buga misalin wani yaro mai suna Auwalu Biliya daga ƙaramar hukumar Shinkafi wanda aka ce ya kamu da matsananciyar cutar bayan shan gurɓataccen ruwa da abinci.

Kakarsa, Rakiya Usman, ta ce an fara kai shi asibiti a Shinkafi kafin daga bisani a tura shi babban asibitin Zurmi domin yi masa tiyata bayan hanjinsa ya fashe sakamakon rashin samun kulawa da wuri.

MSF ta ce jinkirin fara magani kan sa cutar ta tsananta har ta kai ga fashewar hanji, abin da ka iya jawo mutuwa idan ba a yi tiyata cikin gaggawa ba.

Baya ga matsalar cututtuka, ƙungiyar ta ce damina na zuwa ne a daidai lokacin da abinci ke ƙarewa a gidaje, lamarin da ke ƙara yawan yara masu fama da tamowa.

A cewar ƙungiyar, ta kula da yara 60,566 masu fama da tamowa a Zamfara cikin shekarar 2025, inda yara ‘yan ƙasa da shekara 15 da mata masu juna biyu suka fi shiga haɗari.

Kazalika, MSF ta kuma nuna damuwa kan yadda rashin tsaro, rushewar hanyoyi da gadoji sakamakon ambaliya, da tsadar sufuri ke hana mutane isa asibitoci cikin lokaci.

Ƙungiyar ta bukaci a ɗauki matakan kariya cikin gaggawa da suka haɗa da samar da tsaftataccen ruwa, inganta muhalli, ƙarfafa alluran rigakafi da kuma samar da ingantattun cibiyoyin lafiya domin rage mace-mace a lokacin damina.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata