DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Monday, September 14, 2026
HomeSiyasa'Ka rufe bakinka idan ’yan siyasa na magana' - Amaechi ga Sowore

‘Ka rufe bakinka idan ’yan siyasa na magana’ – Amaechi ga Sowore

An yi musayar kalamai mai zafi tsakanin tsohon gwamnan jihar Rivers kuma tsohon ministan sufuri, Rotimi Amaechi, da ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar AAC, Omoyele Sowore, yayin wani zaman tattaunawa a babban taron shekara-shekara na ƙungiyar lauyoyin Nijeriya, NBA, karo na 66 a Port Harcourt.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito rikicin ya samo asali ne bayan Sowore ya kalubalanci tarihin wasu ’yan siyasa da suka taɓa rike mukaman gwamnati, yana mai cewa bai kamata waɗanda suka gaza yayin da suke kan mulki su sake neman amincewar ’yan Nijeriya ba tare da sun yi bayani kan abin da suka aikata a baya ba.

Ya kuma soki ayyukan Amaechi a lokacin da yake gwamnan Rivers da ministan sufuri, tare da ambaton tsohon gwamnan Anambra, Peter Obi a matsayin waɗanda suka yi wasa da damarmakin da suka samu jihohinsu.

Sai dai Amaechi, wanda ya wakilci ɗan takarar shugaban ƙasa na jamiyyar ADC, Atiku Abubakar, ya ƙi amincewa da zargin Sowore.

Inda ya ce kamata ya yi a tantance shi bisa ayyukan da ya gudanar, yana mai ambaton gina hanyoyi, makarantun firamare da kuma ayyukan layin dogo irin su Lagos-Ibadan da Abuja-Kaduna.

Yayin da muhawarar ta ƙara zafi, Amaechi ya ƙalubalanci Sowore da ya nuna irin ƙwarewarsa a shugabanci, sannan ya nemi lauyoyin jihar Rivers su zagaya da shi domin ya ga ayyukan da gwamnatinsa ta gudanar.

Daga bisani ya kalli Sowore, ya ce da shi idan ’yan siyasa na magana, ya rinka rufe bakinsa, domin a cewarsa haryanzu shi ɗan koyo ne.

Taron NBA na bana mai taken “Beyond Limits” yana gudana ne a Port Harcourt daga 21 zuwa 28 ga watan Agusta, inda manyan ’yan siyasa da lauyoyi ke tattauna batutuwan shugabanci, manufofin gwamnati da makomar Nijeriya gabanin babban zaɓen 2027.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata